Dalibai 1.59m da sauran abubuwa 6 a kan sakamakon jarabawar WAEC ta bana
Hukumar shirya jarawabar kammala karatun sakandire Yammcin Afirka WAEC (West African Examination Council), ta saki sakamakon jarabawar bana ta 2019 a ranar Juma'a 26 ga watan Yuli.
Shugaban hukumar na reshen Najeriya, Mista Olu Adenipekun, shi ne ya labartawa manema labarai wannan rahoto cikin wata sanarwa yayin ganawa da su a ofishin hukumar dake unguwar Yaba a jihar Legas.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, dalibai 1,590,173 ne suka zana jarabawar a bana a makarantun sakandire 18,639 da hukumar ta yarjewa a fadin Najeriya.
Ga wasu muhimman ababe shida da babu lallai ku na da masaniyarsu game da sakamakon jarabawar bana da hukumar WAEC ta saki.
1. Hukumar WAEC ta rike sakamakon jarabawar dalibai 180,205 a fadin Najeriya
2. Dalibai 1,596,161 ne suka yi rajistar jarabawar WAEC a bana. Sai dai dalibai 1,590,173 ne kacal suka zana jarabawar da aka gudanar a cikin watan Mayu da Yunin 2019.
3. Cikin dalibai 1,590,173 da suka zana jarabawar a bana, 822,098 sun kasance dalibai maza yayin da 768,075 suka kasance mata.
4. Kaso 68.18 cikin 100 da suka zana jarabawar a bana, sun yi nasarar samun Credit biyar da suka hadar da darussan lissafi da kuma turanci wato English da Mathematics.
5. Dalibai mata sun kasance masu mafi rinjayen kaso na samun nasara fiye da 'yan uwan su dalibai maza kamar yadda alkalumma na hukumar suka zayyana.
KARANTA KUMA: Firaiministocin Birtaniya 13 da suka yi zamani da sarauniyar Ingila, Elizabeth
6. Mata 517,657 sun yi nasarar samun Kiredit biyar da suka hadar da darussan lissafi da kuma turanci fiye da adadin maza 507,862 da suka samu makamanciyar wannan nasara.
7. An samu karuwar nasara da kaso 14.18 a kan kaso 50 cikin 100 da ta kasance a sakamakon jarabawar bara ta 2018.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng