To fah: Sai nafi kowacce jarumar Kannywood shahara a duniya - Jaruma Maryam MJ

To fah: Sai nafi kowacce jarumar Kannywood shahara a duniya - Jaruma Maryam MJ

- Sabuwar jaruma mai tasowa Maryam MJ ta bayyana cewa sai ta fi kowacce jaruma mace suna a masana'antar Kannywood matukar Za a bata dama

- Jarumar ta ce duk jaruman da suka yi suna a masana'antar irinsu Rahama Sadau, Nafisa Abdullahi, Hadiza Gabon da sauransu, duk sun kai wannan matsayi ne saboda damar da aka basu

- Ta kuma yi kira ga masoyansu da su dinga yi musu kyakkyawan zato da fatan alkhairi a wannan sana'ar da suke yi

Sabuwar jaruma mai tasowa Maryam MJ ta sha alwashin cewa sai tafi kowacce jaruma mace tashe da shuhura a masana'antar Kannywood matukar za a bata dama ta nuna irin basirar ta kamar yadda ake bawa sauran jarumai mata.

Jarumar ta yi wannan ikirari ne a wata tattaunawa da akayi da ita inda take bayyana cewa ba komai ne yasa jarumai mata irin su Rahama Sadau, Hadiza Gabon, Aisha Tsamiya da sauran su suka kai matakin da suke yanzu ba sai damar da ake basu na shirya fina-finai akai akai, inda ta tabbatar da cewa matukar ta samu dama irin wannan za a sha mamakinta watakila ma ta fisu shahara.

Maryam ta bayyana darakta Sunusi Oscar a matsayin ubangidanta wanda ya fara sanya ta a cikin wannan sana'a ta fim wanda zata iya kiransa a matsayin tsaninta na taka dukkan matakan da zata taka a gaba.

KU KARANTA: Bidiyo: Masu yi mana zargin madigo sai mun rigaku shiga Aljanna - Layla kawar Hadiza Gabon

Jarumar 'yar asalin jihar Adamawa Bafulatanar asali ta bayyana cewa yanzu haka tana karatu ne a kwalejin tarayya dake Bauchi, inda take karatu a bangaren kasuwanci, kuma tana karatune tana hadawa da sana'ar fim.

Haka zalika jarumar ta kara da cewa ita sana'ar fim ta dauke ta a matsayin sana'a ce kuma ta bata muhimmanci matuka domin babu irin matakin da za a bata batare da ta taka rawa akai ba matukar bai sabawa addini ba, amma ko menene za ta yi.

A yanzu haka jarumar ta fito a bidiyon wakoki da yawa, inda nan gaba kadan kuma za ta fara fitowa a fina-finan da za ta taka rawa a ciki sama da guda biyar da suke kan hanyar fitowa nan ba da jimawa ba, kuma yanzu haka suna shirin fara daukar wani sabon fim mai suna Meemah wanda darakta Sunusi Oscar zai bayar da umarni.

A karshe dai jarumar tayi kira ga masoyansu da su dinga yi musu kyakkyawan zato da fatan alkhairi akan sana'ar da suke yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng