Bidiyo: Masu yi mana zargin madigo sai mun rigaku shiga Aljanna - Layla kawar Hadiza Gabon

Bidiyo: Masu yi mana zargin madigo sai mun rigaku shiga Aljanna - Layla kawar Hadiza Gabon

- An nuno Laila kawar Hadiza Gabon ta na daukar bidiyon kanta tana yiwa mutane da suke yi musu zargin cewa su 'yan madigo ne ita da kawarta

- Kwanakin baya dai magana ta yadu a kafafen sada zumunta inda ake zargin kawayen da cewa madigo suke yi shine yasa kawancensu kullum yake kara karfi

- Laila ta bayyana cewa wallahi duk mutanen da suke musu kazafin nan sai ta riga su shiga Aljannah

An nuno Laila kawar fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa na Kannywood wato Hadiza Gabon, a wani bidiyo ta na yiwa mutanen da suke yi musu zargin cewa su 'yan madigo ne ita da kawarta Hadiza Gabon.

Kwanakin baya dai an zargi kawayen guda biyu da cewar kawancen sun yana da wata manufa, ma'ana suna wani abu ne da ya san kawancen su yake kara karfi, wasu kuma kuru-kuru sun fito sun bayyana cewa kawayen 'yan madigo ne.

KU KARANTA: Tashin hankali: Kowanne dare sai aljani ya zo ya sadu dani ta baki - Wata mata ta kai kuka wajen Fasto

Ga dai abin da Laila take cewa a cikin bidiyon din:

"Assalamu Alaikum, ina fatan kowa yana lafiya, magana ce dama zanyi akan mutanen da suke yi mana zargin cewa mu 'yan madigo ne, saboda a gaskiya ina jin tausayin mutanen da zasu shiga wuta a dalilina.

"Mutane kuna kallo zan shiga Aljannah, Wallahi Tallahi sai na riga ku shiga, saboda ni na sani ina ji a jikina, irin mu ne zamu wuce kamar walkiya, sai dai ka jiyo mutane suna wacece waccan, ya za ayi Laila ta shiga bayan ita 'yar iska ce.

"Maganar gaskiya shine, mutane ku dai na yiwa mutane kazafi kuna shirya abu haka kawai baku jiba baku gani ba, saboda akwai ranar kin dillanci.

"Wani abu kuma da baku sani ba shine, yawan maganar mu da kuke yasa mutane yanzu suna tururuwar su san ko su waye mu, hakan yasa muna kara yin suna a duniya.

"Kun san ni ina da zuciya mai kyau, hakan ne ma yasa nake ta tunanin yadda a karshe zaku je kuji kunya ranar tashin kiyama, wallahi sai Allah ya saka mana akan duk abinda kuka fada a kanmu.

"Ni ba zanyi zagi ba, duk wadanda suka fada har maganar ta zo kunnena na yafe musu, amma dai ina sanar daku cewa wallahi sai na riga ku shiga Aljannah."

Ga bidiyon da tai a kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel