Australiya ta fi kowace kasa yawan mafi karancin albashin Ma’aikata

Australiya ta fi kowace kasa yawan mafi karancin albashin Ma’aikata

Jaridar nan ta The Economist ta Duniya ta kawo wani rahoto inda ta bayyana jerin kasashen da ma’aikatansu ke samun albashi mai tsoka. Ta farko a wannan jerin tun ba yau ba ita ce Australiya.

Kasar Australiya ta dade da yin kaurin-suna wajen biyan ma’aikata mafi karancin albashi da ya kere ko ina a Duniya. Asali ma kasar ce ta biyu da ta fara yanke mafi karancin albashin ma’aikata.

A shekarar 1896 Australiya ta shigar da kudiri a majalisa inda a ka kayyadewa ma’aikata mafi karancin albashin da za su karba. A wancan lokaci kasar New Zealand ce kadai ta kai ga haka.

A kasar ta Australiya kowane ma’aikaci ya na tashi da Dala 14.14 idan ya yi aikin sa’a guda. Hakan na nufin a kudin Najeriya, ma’aikacin kasar zai samu abin da ya haura N4900 a cikin awa daya.

KU KARANTA: Za a fara biyan ma'aikata mafi karancin albashin N30, 000 a Najeriya

Kasashen da ke biye su ne: Luxembourg inda mafi karancin kudin aikin sa’a guda ya ke $13.14. A New Zealand da Faransa kuwa, kowane Ma’akaci zai karbi abin da bai gaza $11.28 da $11.24 ba.

Ma’aikatan kasar Faransa, Jafan, Amurka, Koriya ta Kudu, Malta, Sifen, Portugal, Foland, Girka, Istonia da Sulobania su na cikin wannan sahu na kasashen da ke biyan ma’aikata kudi mai tsoka.

Ga dai jerin kasashen da su ka zarce kowane wajen biyan ma’aikata:

1 Australiya

2 Luxembourg

3 New Zealand

4 Faransa

5 Netherlands

6 Ireland

7 Belgium

8 Jamus

9 Birtaniya

10 Kanada

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel