Yadda aka kusa yi min auren dole, lokacin ina 'yar shekara 13 - Jaruma Rahama Sadau
- Fitacciyar jaruma Rahama Sadau ta bayyana wani boyayyen sirri na rayuwarta
- Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin da ake yi mata tambaya dangane da yadda za a kawo karshen auren wuri da ake yiwa yara mata a yankin Hausa
- Ta bayyana cewa lokacin da take 'yar shekara 13, iyayenta sun so suyi mata auren dole
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood, Rahama Sadau, wacce yanzu haka take taka muhimmiyar rawa a fina-finan Kudancin Najeriya na Nollywood, ta bayyana wani sirri dangane da rayuwarta.
Bayan wata tambaya da aka yiwa jarumar akan hanyoyin da za abi a kawo karshen auren wuri da ake yiwa yara mata a nahiyar Hausa ta arewacin Najeriya, jarumar ta bayyana cewa ko ita ma an so ayi mata aure lokacin tana'yar shekara 13 a duniya.
"Mutane da yawa suna yin iya bakin kokarinsu wurin bayyana illar auren wuri da ake yiwa yara mata, amma matsalar abu ne wanda an jima ana yin shi, kuma yanzu da mutum ya fara maganar Malaman Addini za su yi caa a kanshi.
KU KARANTA: Ke duniya: An gano wani katafaren shago da ake sayar da sassan jikin mutum, an kuma binciko gawarwakin mutane da aka yanka a cikin shagon
"A bangarena ina yin kokarin zama da iyayen yaran na yi musu bayani akan illolin. Ko ni nan da kuke gani an so ayi mini aure lokacin ina 'yar shekara 13.
"Ina yiwa mahaifiyarmu jinjina domin ita ce kullum take kokari wajen ganin mun zama wasu a rayuwa."
Rahama Sadau dai ita ce fitacciyar jarumar Hausan nan da aka kamata da laifin yin waka da rungume-rungume da wani mawaki dan garin Jos a shekarar da ta gabata.
Jarumar ta samu kyaututtuka kala-kala a bangaren wasanni. Ta samu kyautar gwarzuwar shekara a shekarar 2014, sannan ta kara samun kyautar a shekarar 2015. Sannan ta lashe gasar gwarzuwar Afirka a shekarar 2015.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng