Dalilin da ya sa muke sulhu da 'yan bindiga - Gwamna Tambuwal

Dalilin da ya sa muke sulhu da 'yan bindiga - Gwamna Tambuwal

Gwamnatin Jihar Sokoto ta ce tana tattaunawa da 'yan bindiga da sauran wadanda suke kai hare-hare da iyakar jihar ta.

Direkta Janar na Yadda Labarai da Hulda da Jama'a na Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Abubakar Shekara ne ya bayyana wa Daily Trust hakan jiya Alhamisa a garin Sokoto.

A cewar Shekara, an fara ganin amfanin tattaunawar da ke yi inda 'yan bindigan suka fara sako wasu mutane da su kayi garkuwa da su a ranar Talata.

"Muna sa ran za a samu nasarar idan aka cigaba da sulhun duba da cewa 'yan bindiga da dama da shugabanin su sun amince za su ajiye makamansu," inji shi.

KU KARANTA: El-Zakzaky: Sheikh Ahmad ya fadawa gwamnati yadda za a magance matsalar 'yan shi'a

Ya yi kira ga mutanen da su ke barin kauyukansu saboda tsoron hari a sassan jihar su zauna a gidajensu saboda 'yan bindigan sun tabbatarwa gwamnati cewa za su dakatar da kai hare-hare.

Shekara ya kuma yi kira ga al'ummar jihar su guji cin mutuncin 'yan uwansu makiyaya Fulani a garuruwa da kasuwanin kauye.

"Ya zama dole mu cigaba da zaman lafiya kamar yadda aka san mu da shi," inji shi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa al'ummar kauyukkan Isa da Sabon Birni a karamar hukumar Goronyo duk sun tsere saboda yawan hare-haren da 'yan bindigan ke kai musu.

Rahotanni sun bayyana cewa a kalla mutane 60 ne 'yan bindiga suka kashe a jihar Sokoto a wannan shekarar. An kashe 26 a watan Janairu a garin Gandi da ke karamar hukumar Rabah.

A watan Fabrairu kuma an kashe wasu mutane 16 a Dalijan, Rakkoni da Kalhu duk dai a karamar hukumar Rabah. Daga baya-bayan nan kuma an kashe mutane 20 a Kamitau Mala Faru da Dan Tatsoko a karamar hukumar Goronyo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel