Zamanin sayen bayi akan dutse muka kari rayuwar mu, kuma bamu da addini da ya wuce bautar dodo - Sarkin Ma'as

Zamanin sayen bayi akan dutse muka kari rayuwar mu, kuma bamu da addini da ya wuce bautar dodo - Sarkin Ma'as

A wata ziyara da wakilin mu Sani Hamza Funtua ya kai kauyen Ma'as dake cikin jihar Bauchi, yayi tattaki har zuwa fadar mai garin kauyen, inda yayi hira da shi

Funtua ya yiwa mai garin tambayoyi kala-kala, inda suka shafe kusan mintuna goma suna hira a tsakaninsu.

A cikin hirar ne mai garin yake bayar da tarihi garin da kuma yadda aka yi garin ya habaka zuwa wannan lokaci.

Ga yadda hirar ta su ta kaya:

Ranka ya dade ko zaka dan yi mana takaitaccen bayani akan wannan gari na Ma'as?

Mu dai mutanen garin Ma'as ba zuwa muka yi ba dama can mu mutanen Bauchi ne, da muna zaune a kan duwatsu ne bamu sakkowa har sai da aka daina sana'ar sayar da bayi sannan muka sakko, daga sakkowarmu zuwa yanzu yafi shekara dari.

Lokacin da muke kan dutse bamu da addini, sai daga baya Allah ya kawo mana addini, wasu suka shiga musulunci wasu kuma suka shiga kiristanci, yanzu dai babu wanda yake bautar gunki ko dodo a cikinmu.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta yaudare ni - Tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Hon Bashir Garba Lado

Zaka iya yi mana bayani akan batun wutar lantarki a wannan kauyen?

Mu bamu taba samun wutar lantarki ba sai dai mu gani a garin mutane, misali idan mun shiga birni ko kuma wasu garuruwa da suke makwabtaka damu wadanda suke da wuta.

Mun sha zuwa mu roki gwamnati akan ta kawo mana dauki akan halin da muke ciki, amma har yanzu babu wani canji da muka samu.

Ya zancen ilimin boko da addini a garin nan?

Kwarai muna da makarantar firamare a garin nan, sannan kuma akwai makarantar addini, malaman da ke koyar da yaran namu sukan zo daga cikin garin Bauchi da kuma wasu garuruwa dake makwabtaka damu.

Ya maganar ruwan sha, kuna samun mai tsabta kuwa?

Da an zo an haka mana burtsate, munyi amfani dashi na tsawon shekara shida, amma tunda barayi suka zo suka sace muka shiga matsalar ruwan sha a wannan kauyen namu, mun kai kukanmu ga karamar hukuma, amma babu wani abu da aka yi.

Ya harkar siyasa, shin kuna da wurin kada kuri'a a garin nan?

Kwarai kuwa tun lokacin shugaban farar hula na farko muke kada kuri'a a garin nan har zuwa yanzu, kowacce siyasa damu ake gwabzawa. Sai dai kawai zasu zo su cika mu da surutun iska amma ba wani alkawari da suke cikawa idan sun dauka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng