Rainin hankali: An kama dan kasar Amurka yana casa dan Najeriya a Legas saboda yana aikinsa

Rainin hankali: An kama dan kasar Amurka yana casa dan Najeriya a Legas saboda yana aikinsa

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya dake aiki a filin sauka da tashin jirage na jahar Legas sun kama wani bature dan kasar Amurka bayan ya sharara ma wani dan Najeriya mari yayin da yake bakin aikinsa, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 24 ga watan Yuli yayin da jami’an dake kula da ababen hawa a filin jirgin suka nemi su kama motar dan Amurkan mai suna Breedlove Shawn dan shekara 52 saboda ya ajiye motarsa a inda bai kamata ba.

KU KARANTA: Yan fashi sun kai hari wata ma’aikata, sun yi awon gaba da makudan kudade

Sai dai cikin fushi dan Amurka ya fito daga motarsa, inda ya wanka ma jami’in mari, kamar yadda manajan kamfanin kula da ababen hawan, Alhaji Lamidi Falekulo ya tabbatar ma manema labaru.

Majiyarmu ta tuntubi DPO na Yansandan filin jirgin, Danjuma Garba don jin ta bakinsa, inda ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuam yace a yanzu haka suna tsare da wannan bature Breedlove Shawn.

“Da gaske ne mun kamashi, kuma da zarar mun kammala gudanar da bincike zamu gurfanar dashi gaban kuliya manta sabo a kan tuhumarsa da cin zarafin dan Adam tare da raunatashi.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wani matashi dan shekara 25 mai suna Rilwan ya yi ma wata jami’ar Yansanda satar kudi naira na gugan naira har N62,000 a ofishin Yansanda dake Agege, cikin garin Ikeja na jahar Legas.

Matashi mai karfin hali ya bude teburin Yarsandan ne yayin da yake rike a ofishin, inda ya saci kudin, amma wani jami’in Dansanda ya ga lokacin daya dauki kudin, don haka dubunsa ta cika, tuni Yansanda suka mikashi gaban kotu don fuskantar hukuncin sata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel