Sabo Nanono: Abinda ya kamata ku sani game da zababen Ministan Buhari daga Jihar Kano

Sabo Nanono: Abinda ya kamata ku sani game da zababen Ministan Buhari daga Jihar Kano

A yau Talata 23 ga watan Yuli ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen mutane 43 da ya zaba domin nadawa a matsayin ministoci a mulkinsa zango na biyu.

Jihar Kano tana daya daga jihohin da Shugaban Kasa ya zabi mutane biyu domin nada su a matsayin ministoci wadanda suka hada da Alhaji Sabo Nanono da Manja Janar Bashir Salihi Magashi (murabus).

Kamar yadda ya bayyana a hirar da aka yi da shi, Alhaji Muhammad Sabo Nanono ya ce an haife shi ne a garin Tofai da ke yankin Zakirai na karamar hukumar Gabasawa ta jihar Kano a ranar 11 ga watan Afrilun 1946.

DUBA WANNAN: Janar Magashi: Abinda ya kamata ku sani game da zababben ministan Buhari daga jihar Kano

Alhaji Nanono ya yi karatun frimare a garin Zakirai da Gwarzo. Ya yi karatun sakadire a kwallejin gwamnati da ke Kano daga nan kuma ya cigaba zuwa Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya yi karatun digiri a fanin kasuwanci ya kuma kamalla a 1972.

Har ila yau, Nanono ya yi digiri na biyu a Jami'ar Wisconsin da ke Amurka. Ya kuma yi kwas a makarantar nazarin kasuwanci ta Harvard a Boston Massachusetts a shekarar 1994.

Ya yi aiki a matsayin malami a makarantun gaba da sakadire, ya yi aikin banki inda har ya kai matsayin Manajin Direkta daga bisani kuma ya tsinduma siyasa da aikin noma.

Alhaji Sabo Nanono (Dagajin Tofai) ya hallarci kwasa-kwasai da dama a gida Najeriya da kasashen ketare kuma shi mamba ne na kungiyoyin kwararu masu yawa a kasar. Yana kuma da matan aure da 'ya'ya 11.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel