Yan sanda vs Yan Shi'a: Anyi sabuwar lalle a yau, an kashe mutane 2, da dama sun jikkata

Yan sanda vs Yan Shi'a: Anyi sabuwar lalle a yau, an kashe mutane 2, da dama sun jikkata

Kwana biyu kenan ana zub da jini a birnin tarayya Abuja yayinda yan kungiyar IMN wadanda akafi sani da yan Shi'a suka sake gwabzawa da jami'an yan sandan Najeriya a zanga-zangar da suka gudanar a shahrarriyar kasuwar Banex dake Wuse Abuja.

Bisa ga rahoton da yan sandan suka samu cewa yan Shi'an zasu fito yau misalin karfe 2 na rana, sai suka tare hanyar domin hanasu.

Wani mai idon shaida ya bayyanawa manema labarai cewa rikici ya fara ne lokacin da yan Shi'an suka fara jifan yan sanda da duwatsu.

Sakamakon hakan ya sa yan sanda suka fara harbinsu da harsasai da barkonon tsohuwa domin tarwatsasu, a yayin haka aka hallaka yan Shi'a biyu.

Wannan abu ya tayar da hankulan yan kasuwa, ma'aikata, direbobi, a unguwar Wuse wanda ya kai ga yan kasuwar suka fara kulle shagunansu.

Yan Shi'an sun lalata motoci jama'a da aka ajiye a kan hanya.

A labari mai kama da haka, Akalla yan sanda biyar sun rasa rayukansu a rikicin jami'an tsaro da yan kungiyar IMN wanda aka fi sani da Shi'a a ranar Litinin, 22 ga watan Yuli, 2019 a birnin tarayya Abuja.

Wannan ya hada da babban jami'in hukumar mai kula da ayyukan birnin tarayya, DCP Usman Umar, wanda yan Shi'a suka harba yayinda yake kokarin hanasu tare hanyar tafiyan motoci da yan kasuwa.

Bayan mutuwarsa, sauran yan sandan ke suka jikkata a asibiti suka kwanta dama.

Hakazalika, Ma'aikacin gidan talabijin Channels, Precious Owolabi, wanda harsashi ya samu yayin rikici tsakanin yan Shi'a da yan sanda a birnin tarayya Abuja ya rigamu gidan gaskiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel