Allahu Akbar: Mahaifiyar Shuaibu Mikati mai shekaru 80 ta rasu

Allahu Akbar: Mahaifiyar Shuaibu Mikati mai shekaru 80 ta rasu

Mun samu labarin rasuwar Mahaifiyar wani babban ‘dan siyasa da ya yi fice a jihar Kaduna. Wannan ba kowa ba ne illa Alhaji Shuaibu Idris (wanda a ka fi sani da Mikati).

Shuaibu Idris Mikati wanda ya yi takarar gwamnan jihar Kaduna a zaben da ya gabata ya rasa Mahaifiyar ta sa ne mai suna Hajiya Abida (Goma) a yau 23 ga Watan Yuli, 2019.

Hajiya Abida wanda mutane su ka fi sani da Hajiya Goma ta rasu ne ta na mai shekaru 80 a Duniya. Kamar yadda Daily Trust, ta rahoto, Goma ta rasu ne a cikin karamar hukumar Giwa.

Rahotanni sun nuna cewa Hajiya Abida ta yi fama da doguwar rashin lafiya wanda a karshe cutar ta yi sanadiyyar ajalinta. Marigayiyar ta yi jinya na wasu ‘yan watanni a gidan ta.

KU KARANTA: Kwankwaso ya yi wa manyan 'yan siyasan Kaduna ta'aziyya har gida

Wani babban Aminin ‘dan siyasar mai suna Alhaji Ibrahim Danshehu, ya bayyanawa Manema labarai labarin cikawar wannan Dattijuwa lokacin da ya zanta da su a Garin Kaduna.

Daga cikin ‘Ya ‘yan na ta akwai shi Alhaji Shuaibu Idris Mikati mai shekaru 55 a Duniya. Marigayiyar ta haifi Shuaibu Mikati ne a Garin Dogon Dawa da ke cikin Birnin Gwari.

Idan ba ku manta ba daga cikin wadanda su ka nemi kujerar gwamnan Kaduna a PDP tare da Shuaibu Idris Mikati akwai Ramallan Yero, Alhaji Isah Ashiru, Mohammed Sani-Bello.

Sauran Abokan takararsa sun hada da ; Mohammed Sidi; Suleiman Hunkuyi; da Jonathan Kish. Alhaji Shuaibu Idris Mikati ya rike mukamai da-dama har a kamfanin Aliko Dangote.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel