El-Zakzaky: Hadimar Buhari ta fadi kasar da ke bawa 'Yan Shi'a tallafin Kudi

El-Zakzaky: Hadimar Buhari ta fadi kasar da ke bawa 'Yan Shi'a tallafin Kudi

Hadimar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie ta yi ikirarin cewa kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) da aka fi sani da Shi'a suna samun tallafin kudade ne daga kasar Iran.

Onochie ta bayyana hakan ne a shafin ta na sada zumunta na Twitter a ranar Talata 23 ga watan Yulin 2019.

Wannan zargin na Onochie ya biyo bayan wata kazamar zanga-zanga da 'yan kungiyar suka gudanar a babban birnin tarayya Abuja wadda ta yi sanadiyar rasuwar mataimakin kwamishinan 'Yan sanda mai kula da sashin ayyuka na Abuja, Usman Umar, Dan jaridar Channels TV, Precious Owolabi da kuma wasu matasa da akayi ikirarin 'yan Shi'a ne.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An sake yin gumurzu tsakanin jami'an tsaro da 'Yan Shi'a a Abuja

Duk da cewa Onochie ta ba bayyana wasu kwararran hujoji kan ikirarin da ta yi ba, akwai yiwuwa goyon bayan da gwamnatin Iran ke bawa 'yan Shi'an ne ya sanya tayi wannan ikirarin.

A shekarar 2016, Gwamnatin Iran tayi tsokaci kan cigaba da tsare El-Zakzaky inda ta ce hakan ya sabawa doka kuma ba adalci bane.

Sakon ya fito ne daga bakin tsohon wakilin kasar a Najeriya, Saeed Koozechi inda ya ce matsayar gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran shine bai dace a cigaba da tsare El-Zakzaky na lokaci mai tsawo ba.

"'Yan Shi'a kungiya ce mara rinjaye a Najeriya kuma suna yin ibadun su ne cikin zaman lafiya da lumana, ba su barazana ga zaman lafiyar kowa," a cewar Koozechi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel