An sake kwatawa: Yan bindiga sun sace mata dayawa sun kashe mutane 15 a jahar Katsina

An sake kwatawa: Yan bindiga sun sace mata dayawa sun kashe mutane 15 a jahar Katsina

Akalla mutane 15 ne suka gamu da ajalinsu yayin wani mummunan hari da wasu gungun yan bindiga suka kai wani kauyen Zango dake cikin karamar hukumar Kankara ta jahar Katsina, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun kai ma kauyen farmaki ne da yammacin lahadi, 21 ga watan Yuli, kamar yadda wani mazaunin kauyen ya tabbatar, inda yace yan bindigan sun yi awon gaba da yan mata da dama.

KU KARANTA: Fadan yan Shia da Yansanda: Buhari ya shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro

“Yan bindigan sun banka ma gidan dakacin kauyenmu wuta, sa’annan sun kona motarsa. Daga nan kuma suka yi awon gaba da mata dama zuwa cikin daji.” Inji shaidan gani da ido daya nemi a sakaya sunansa.

Sai dai rundunar Yansandan jahar bata tabbatar da aukuwar lamarin ba, inda kaakakin rundunar, Gambo Isah ya bayyana cewa basu samu rahoton harin ba, har sai ya tuntubi DPO na Yansandan yankin kafin ya samu tabbaci ko akasin hakan.

“Har yanzu ina sauraran rahoto daga DPO na Yansandan karamar hukumar Kankara.” Inji shi.

A wani labarin kuma, zaman lafiya ya fara samuwa a jahar Zamfara sakamakon sulhu da gwamnan jahar, Bello Matawalle ya fara yi da yan bindiga, inda a yanzu haka sun sake sako mutane 143 da suka yi garkuwa dasu.

Idan za’a tuna, a baya, jahar Zamfara ta yi kaurin suna wajen matsalar tsaro, inda ake yawan samun hare haren yan bindiga, satar shanu, garkuwa da mutane, wanda hakan ya sanya rashin amince tsakanin Fulani da Hausawa, tare da janyo asarar rayuka da dimbin dukiya.

Sai dai sabon gwamnan jahar Zamfara, Gwamna Matawalle ya zo da sabon salo, inda ya ga dacewar gudanar da zaman tattaunawa na sulhu tsakanin yan bindigan da gwamnati, da kuma yan kato da gora, kuma zuwa yanzu hakan bada sakamako mai kyau.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel