'Yan bindiga sun dauke Turkawa 4 a jihar Kwara

'Yan bindiga sun dauke Turkawa 4 a jihar Kwara

Wani mummunan rahoto dake zuwa mana a yanzu da sanadin jaridar The Nation ya bayyana cewa, 'yan bindiga dadi sun yi awon gaba da wasu Turkawa hudu a wata mashaya dake kauyen Gbale na karamar hukumar Edu a jihar Kwara.

Wannan lamari ya auku da misalin karfe 10 na daren Asabar, 20 ga watan Yuli, yayin da mazajen hudu 'yan asalin kasar Taki ke sharholiyar su a wata karamar mashaya cikin kauyen jihar Kwara a Arewa ta Tsakiya.

Jaridar The Nation ta wassafa sunayen su tare da shekarun haihuwa kamar haka; Yasin Colak (33), Senerapal (40), Ergun Yurdakul (35) da kuma Seyit Keklik (25).

Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen hudu da azal ta afkawa sun kasance ma'aikatan wani kamfanin gine-gine dake kauyen Gbale mai sunan Istanbul Concrete Limited.

Kakakin rundunar 'ya sandan Najeriya reshen jihar Kwara, Ajayi Okansami, yayin ganawar sa da manema labarai ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari.

KARANTA KUMA: Sauran kiris ta'addancin 'yan daban daji ya zama tarihi a jihar Katsina - Masari

Kazalika kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Kayode Egbetokun, ya bayar da umurnin gaggauta fara bincike domin bankado miyagun dake da hannun cikin wannan muguwar aika-aika, tare da kubutar da mutanen hudu ba tare da rayukan su sun salwanta ba.

A wani rahoton mai nasaba da wannan, cikin watan Afrilun da ya gabata ne wasu bakin haure biyu 'yan kasar Scotland da kuma Canada, suka afka tarkon masu ta'adar garkuwa da mutane a yankin Abua na Kudancin jihar Ribas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng