Kwallon kafa: Gareth Bale zai bar Real Madrid Inji Koci Zidane

Kwallon kafa: Gareth Bale zai bar Real Madrid Inji Koci Zidane

Kungiyar kwallon kafa na Real Madrid da ke Sifen ta tabbatar da shirinta na rabuwa da babban ‘Dan kwallonta Gareth Bale bayan da Mai horas da kungiyar ya nuna ba zai sake amfani da shi ba.

Zinedine Zidane wanda shi ne Kocin Real Madrid, ya bayyana cewa ya na neman hanyar rabuwa da ‘Dan wasansa Gareth Bale. Zidane ya nuna cewa Bale ya buga wasansa na karshe a Kulob din.

Zidane ya bayyanawa Manema labarai cewa Gareth Bale ya kama hanyar barin Real Madrid, bayan da a ka ajiye shi gaba daya a wasan kawancen da Real ta buga da Bayern Munchen a jiya.

A Ranar Asabar dinnan, 20 ga Watan Yuli, Real Madrid ta buga wasa da babban Kulob din na Jamus. An doka wannan wasa ne a Birnin Houston da ke kasar Amurka babu ‘Dan wasa Bale.

Kocin kungiyar ya ce: “Mu na sa ran ya tattara ya tafi kwanan nan. Wannan ne maslahar da za ta ficewa kowa. Mu na kokarin ganin ta koma wani Kulob.”

“Babu wata kullaliya tsakani na da shi, amma wani lokaci dole sai an dauki matakin da ya dace. Dole mu yi canji.” Inji Zidane.

Kocin ya kara da cewa: “Ban sani ba ko nan da sa’a 24 ko 48, zai tashi, amma na san zai tafi. Wannan ne mafita ga kowa.”

KU KARANTA: 'Dan wasan Najeriya da ya yi ritaya ya ajiye irin tarihin R. Yekini

Wa zai kashe kudi ya saye Gareth Bale?

1. Man Utd

Daga cikin kungiyoyin da a ka tunani za su iya sayen Gareth Bale akwai Manchester United wanda ta dade ta na sha’awar ‘Dan kwallon. Sai dai ba dole bane ta iya kashe kudi ta saye shi a yanzu.

2. Bayern Munich

Haka zalika kungiyar Bayern Munchen za ta iya karbar ‘dan wasan gefen na kasar Wales ganin manyan ‘yan kwallonta; Franck Ribery da Arjen Robben sun tashi daga kulob din a kakar bana.

3. Tottenham

Akwai yiwuwar Gareth Bale ya koma kulob din da ya baro a Landan watau Tottenham a 2013. Ana kishin-kishin din Bale din da a ka saida a fam miliyan €100 zai tashi a miliyan €50 a bana.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel