Yadda wani saurayi ya datse kan budurwarsa bayan sun gama soye wa cikin dare

Yadda wani saurayi ya datse kan budurwarsa bayan sun gama soye wa cikin dare

An gano gawar wata mata mai suna Mama Maria da ake zargin saurayin ta ya datse kan ta a garin Owode da ke karamar hukumar Yewa ta Kudu a jihar Ogun.

Lamarin ya faru ne makonni biyu da suka gabata bayan wani mutum da ba a bayyana sunansa ba ya sadu da marigayiyar.

A cewar majiyar, matar ta sananniya mai sayar da abinci ne a kasuwar Illaro.

Ta gayyaci mutum zuwa gidan ta ne ya yi kwana daya yayin da suka samu rashin jituwa jim kadan bayan sun gama saduwa.

DUBA WANNAN: Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa

An ruwaito cewa mutumin ya makure matar kafin daga bisani ya datse kan ta kuma ya tsere daga gidan.

Da safiya ya yi makwabta suka lura matar ba ta fito daga dakin ta ba kuma suka lura jini na kwararowa daga kofarta sun balle kofar dakin inda suka gano gawarta a dakin tare da kanta a datse.

An bayyana cewa 'Yan sanda sun dauke gawar daga gidan.

Majiyar ta ce: "Mun yi mamakin ganin matar da dawo gida da wani mutum a daren da zai kashe ta.

"Da farko mun ji hayaniya amma daga bisani sai muryansu ya yi kasa hakan yasa mu kayi tsamannin sun sulhunta kansu ne ashe kashe ta ya yi.

"Sai da safe ya yi muka lura ba ta fito da wuri kamar yadda ta saba ba domin gaisawa da makwabta.

"Hakan yasa muka balle kofarta bayan mun lura akwai jini a kasan kofar ta. Mun gano gangan jikinta kwance cikin jini shi kuma saurayin ta an nemi shi an rasa."

Mai magana da yawun 'Yan sanda, Mista Abimbola Oyeyemi ya ce an kama wanda ake zargi da aikata kisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel