Wahalar rayuwa ta sanya mahaifiyar tsohon dan wasan Najeriya Rashidi Yekini fara sayar da biredi a titi
- Rahotanni sun nuna cewa an hango mahaifiyar fitaccen dan wasan kwallon kafar nan Rashidi Yekini ta na sayar da biredi akan titi
- An bayyana cewa tun bayan rasuwar dan wasan, iyalansa sun shiga wata matsin rayuwa inda ya zamanto dakyar suke iya daukar dawainiyar kansu
- A tarihin kungiyar wasan kwallon kafar ta Najeriya dai babu dan wasan da ya kai Rashidi Yekini kafa tarihi dai
Mahaifiyar fitaccen tsohon dan wasan kwallon kafa na kungiyar wasan kwallon kafa ta 'Super Eagles' marigayi Rashidi Yekini ta fara sana'ar sayar da biredi a garin Ila dake jihar Kwara.
Rahotanni sun bayyana cewa tun bayan lokacin da dan nata ya rasu mahaifiyar tare da iyalansa suka shiga halin kaka na kayi, wanda dalilin hakan ya tilasta ta fara sana'ar sayar da biredi, domin samun abin sanyawa a bakin salatinsu.
KU KARANTA: Jerin hanyoyi 24 da shugaba Buhari ke yi a fadin kasar nan
Haka kuma wasu rahotanni sun bayyana iyalan tsohon dan wasan suna cikin wani hali na matsin rayuwa, domin kuwa har mahaifiyar tashi an gani tana neman taimako, saboda yanayin halin da suke ciki.
Idan ba a manta ba a tarihin rayuwar da yayi ta kwallon kafa ya zura kwallaye 37 a cikin wasanni 58 da ya bugawa Najeriya, kuma a lokacin ya kasance dan wasan da yafi yawan kwallaye a kugniyar ta 'Super Eagles'.
Ya kuma jagoranci kungoyar zuwa wasu manyan wasanni guda biyar wadanda suka hada da wasan kwallon kafa na kasar Amurka a shekarar 1994 da kuma wasan kwallon kafa da aka gudanar a kasar Faransa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng