Dandalin Kannywood: General BMB ya cika alkawarin aske gashi saboda nasarar Buhari

Dandalin Kannywood: General BMB ya cika alkawarin aske gashi saboda nasarar Buhari

Shahararren jarumin fina finan Kannywood, Bello Muhammad Bello, wanda aka fi sani da suna General BMB ya cika alkawarin daya dauka na aske tarin gashin dake kansa idan har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe zaben 2019.

Idan za’a tuna a gabanin zaben 2019 ne Bello ya dauki wannan alkawari, inda a baya wani ya taba yi masa tayin zai bashi naira dubu 500 domin ya aske gashin kan nasa, amma yace ba zai yi ba.

KU KARANTA: Askarawan Hisbah sun kama mata masu zaman kansu guda 19 a jahar Jigawa

Dandanlin Kannywood: General BMB ya cika alkawarin aske gashi saboda nasarar Buhari
General BMB ya cika alkawarin aske gashi saboda nasarar Buhari
Asali: Facebook

A makon data gabata ne BMB ya sake hotunansa a kafar sadarwar zamani ta Instagram kansa babu gashi ko daya, ya aske kan kwal, bayan kwashe tsawon shekara 10 yana tara gashin. Kuma yayi haka ne don cika alkawarin daya dauka.

“Wani furodusa ya taba min tayin naira miliyan 1.5 domin na aske gashin kaina na fito a wani shirin fim dinsa, amma kememe na ki, amma a yanzu a shirye nake na aske gashin saboda farin cikin samun nasarar Buhari, wannan zai nuna irin soyayyar da nake yi ma Buhari.” Inji shi.

Jarumin ya aske gashin nasa ne a ranar Juma’a, wanda ta yi daidai da ranar haihuwarsa.

A wani labarin kuma, tsohuwar tauraruwar Kannywood, Hafsat Shehu ta sake dawowa cikin harkar Fim tsundum don cigaba da sana’ar da aka santa dashi, bayan kwashe shekaru 12 tana azumin Fim sakamakon mutuwar mijinta, Ahmad S Nuhu.

Hafsat za ta fito a wani sabon Fim na Adam A Zango mai suna ‘Basaja sabon labari’, kamar yadda aka hangeta a cikin fastan Fim din.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel