Kyakyawan dan sarkin Kano ya kammala karatu daga jami’ar Manchester (hotuna)

Kyakyawan dan sarkin Kano ya kammala karatu daga jami’ar Manchester (hotuna)

- Ashraf Adam Sanusi, dan sarkin Kano, ya kammala karatu kwanan nan daga jami’ar Manchester

- Sarkin ya halarci bikin kammala karatun kyakyawan dan nasa a Ingila

- Ashraf ya baza hadaddun hotuna daga taron a shafinsa na Instagram

Kwanan nan ne Lamido Sanusi, Sarkin Kano ya je kasar Ingila domin taya dansa da ya kammala karatu kwanan nan daga jami’ar da ke Ingila murna. Matashin mai suna Ashraf Adam ya kammala karatu ne daga jami’ar Manchester.

A wajen bikin kammala karatun wanda aka gudanar a ranar 16 ga watan Yuli, abokai, yan uwa da masu fatan alkhairi sun hallara domin taya Ashraf farin ciki.

Kyakyawan matashin ya wallafa hotuna daga taron a shafinsa na Instagram. A rubutun da ya wallaa, ya mika godiya ga dukkanin wadanda suka hallara kan addu’o’insu da kuma kauna.

Kyakyawan dan sarkin Kano ya kammala karatu daga jami’ar Manchester (hotuna)
Kyakyawan dan sarkin Kano ya kammala karatu daga jami’ar Manchester
Asali: Instagram

Kalli hotunan taron a kasa:

KU KARANTA KUMA: Matar mutum kabarinsa: Fasto ya auri budurwarsa mai shekara 63 bayan ta ki shi shekara 50 baya

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya shilla kasar Birtaniya domin ya halarci bikin yaye dalibai da wata jami’ar kasar za ta yi, wanda it ace jami’ar da dansa Fiyinfoluwa ya kammala karatunsa a cikinta.

Babban hadimin Osinbajo a kan harkokin watsa labaru, Laolu Akande ne ya sanar da haka a shafinsa na Twitter, a ranar Laraba, 17 ga watan Yuli.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel