An gudu ba a tsira ba: Saudiyya ta sake gayyato Janet Jackson da 50 Cent su cashe yau a kasar bayan Nicki Minaj taki zuwa

An gudu ba a tsira ba: Saudiyya ta sake gayyato Janet Jackson da 50 Cent su cashe yau a kasar bayan Nicki Minaj taki zuwa

- Yau mawakiya Janet Jackson da kuma mawaki 50 Cent za su cashe a kasar Saudiyya bayan Nicki Minaj taki amincewa ta yi wasa

- Mawakan za su cashe ne a birnin Jeddah na kasar tare da wani mawaki dan kasar Birtaniya da kuma wani Dj daga kasar Amurka

- Nicki Minaj ita ya kamata ace ta jagoranci wannan wasa na mawaka, sai kuma gashi taki amincewa da goron gayyatar kasar, inda ta bayyana cewa kasar basa goyon 'yan luwadi da madigo

Fitacciyar mawakiyar 'Pop' din nan Janet Jackson kanwa a gurin shaharren marigayin mawakin nan Micheal Jackson, ta na daya daga cikin shahararrun mawakan da zasu yi waka a kasar Saudiyya.

Bayan ita kuma akwai shahararren mawakin nan na 'Rap' 50 Cent wanda shima zai je kasar ya baza tashi iyawar. Rahotanni sun nuna a satin da Nicki Minaj ta nuna cewar baza tayi wasan a kasar ba, sai aka gayyato wadannan mawakan guda biyu.

Mawakan za su yi wasan nasu tare da wani mawaki dan kasar Birtaniya mai suna Liam Payne da kuma wani DJ dan kasar Amurka mai suna Steve Aoki a yau Alhamis dinnan a birnin Jeddah.

KU KARANTA: Bayan ya gama sace kayan cocin karkaf, barawon ya rubuta musu takarda akan su yafe mishi laifin satar da yayi

Nicki Minaj ita ce ya kamata ta jagoranci wannan wasa, amma sai ta nuna cewar baza tayi ba saboda rashin nuna goyon bayan 'yan luwadi da madigo da kasar ta Saudiyya take yi.

Nicki Minaj ta yi suna wajen wake-waken batsa da kuma nuna tsiraici a cikin wakokin bidiyonta.

Bayan ta nuna cewa baza tayi wasan ba mutane da yawa sun nuna rashin jin dadinsu a kasar, inda suka dinga zuwa suna karbar kudinsu na shiga wajen wasan.

Sai dai kuma mawakiyar tayi magana a shafinta na Twitter inda ta bayyana cewa ba tayi haka bane dan ta nuna rashin darajar kasar Saudiyya bane.

Haka kuma wata majiyar ta nuna cewa kasar Saudiyyan ce da kanta ta soke zuwan Nicki Minaj din bayan ta yi nazari mai karfi akan cewa bai dace da koyarwar addini da al'adar kasar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng