Amurka za ta kafa manyan kasuwanni a jihohin Najeriya biyu

Amurka za ta kafa manyan kasuwanni a jihohin Najeriya biyu

- Kasar Amurka za ta kafa cibiyoyin kasuwanci na nahiyar Afrika ta yamma a Abuja da jihar Legas

- Darektar cibiyar kasuwanci ta hadin gwuiwa tsakanin Najeriya da Amurka (NACC), Grace Adeyemo, ce ta bayyana hakan

- Adeyemo ta bayyana cewa shirin, da ake son kulla yarjejeniyarsa kwanan nan, zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya

Wakilan gwamnatin kasar Amurka sun ce akwai kyakyawan shirin kafa cibiyoyin kasuwanci na kasashen nahiyar Afrika ta yamma (WATH) a Legas da Abuja da ke Najeriya.

Amurka za ta kafa cibiyoyin ne domin karfafa alakar kasuwanci tsakaninta da Najeriya da kuma ragowar kasashen Afrika ta yamma.

Grace Adeyemo, darektar cibiyar kasuwanci ta hadin gwuiwa tsakanin Najeriya da Amurka (NACC), ce ta bayyana hakan yayin wani taron tattauna kirkiro hanyoyin bunkasa kasuwanci a nahiyar Afrika da gwamnatin kasar Amurka ta dauki nauyinsa.

DUBA WANNAN: Tura ta kai bango: Kungiyar dattijan arewa ta umarci makiyaya su bar kudancin Najeriya

Adeyemo ta bayyana cewa ta na da kwarin gwuiwar cewa kafa cibiyoyin kasuwancin zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya, kuma shirin ya samu goyon bayan shugaban kasar Amurka, Donald Trump.

Sai dai ta ce 'yan kasuwar Najeriya da ke son cin moriyar irin alfanun da kafa cibiyoyin zai zo da su, dole su cika ka'idojin kasuwanci kasa da kasa da Amurka ke amfani da su.

A cewar ta, NACC za ta bayar da shawarwari ga 'yan kasuwar Najeriya da ke son yin amfani da damar da ke cikin yarjejeniyar kasuwancin da za a kulla wajen fitar da kayansu zuwa Amurka domin sayar da su a kasuwannin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Za ka iya aiko mana da labari ta hanyar cike wanna fom da ke kasa:

https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLSch6m8qBDJY3fmT8OH0Dy7Sqkrvwt-tveaPURetOsKjYb_4cQ/viewform

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng