Ran maza ya baci: Ku ajiye makamanku ko kuma ku hadu da balbalin bala'i - Bulama Biu ya gargadi 'yan Boko Haram

Ran maza ya baci: Ku ajiye makamanku ko kuma ku hadu da balbalin bala'i - Bulama Biu ya gargadi 'yan Boko Haram

- Manjo Janar Abdulmalik Bulama Biu ya bukaci 'yan Boko Haram su ajiye makamansu ko kuma su gamu da fushinsa nan ba da dadewa ba

- Biu ya bayyana cewa yanzu yana da wani tsari da idan har 'yan Boko Haram din sun ajiye makamansu ba babu makawa zai karar da su a doron duniya

- Ya ce zai yi amfani da sabon tsarin nasa cikin gaggawa don kawar dasu da kuma dawo da tsaro da kwanciyar hankali a yankin arewa maso gabas

Kwamanda mai lura da rundunar soji ta 7 ta Najeriya dake Maiduguri, Abdulmalik Bulama Biu, ya yiwa 'yan ta'addar Boko Haram wani gargadi akan ko su zo su taya shi murnar karin girman da ya samu ta hanyar ajiye makamansu, ko kuma su hadu da bala'in da basu taba gani ba.

Biu, wanda kwanan nan shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi masa karin girma zuwa mukamin Manjo Janar, ya ce: "Ina sanar da 'yan ta'addar Boko Haram cewa ko su zo su taya ni murnar karin girman dana samu ta hanyar ajiye makamansu ko kuma su shirya yaki dani saboda ina nan zuwa garesu tare da tsarin da zan kawo karshen su."

KU KARANTA: Karshen zancen kenan: Kotu ta bada belin Hanan, matar da ta cakawa mijinta wuka a kahon zuci

Da yake magana da manema labarai, bayan ya dawo daga helkwatar hukumar soji inda aka karrama shi, Biu ya bayyana cewa ya kamata 'yan Boko Haram su hadu da sauran 'yan Najeriya wajen taya shi murna.

Ya bayyana cewa rundunar ta shi yanzu ta gama shiri wajen ganin ta kawo karshen 'yan ta'addar, domin dawo da tsaro da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas.

"Mun gama shiri domin kawo karshen 'yan ta'addar Boko Haram, kuma zamu hakan ne cikin gaggawa, kamar yadda nayi a lokacin da nake bakin aiki," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel