Wata sabuwa: Nade-naden mukaman Gbajabiamila ya kawo sabon baraka a APC

Wata sabuwa: Nade-naden mukaman Gbajabiamila ya kawo sabon baraka a APC

Zabar tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Anambra, Anayo Nnebe da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila yayi a matsayin mai bashi shawara na musamman kan harkokin siyasa na barazana ga hadin kan jam’iyyarsa a yankin kudu maso gabas.

Jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Anambra, sakatarorin labaran APC a kudu maso gabas, da kuma kungiyar matasan APC a kudu maso gabas duk sun yi watsi da zabin, sannan sun yi kira ga maye gurbin Mista Nnebe da wani.

Mista Gbajabiamila a ranar Talata ya sanar da tsohon dan majalisar mai wakiltan Awka ta arewa da kudu a majalisar dokokin jihar Anambra, Mista Nnebe, a matsayin daya daga cikin hadimansa daga yankin kudu maso gabas.

Amma a martani daban-daban da suka yi a ranar Laraba, jam’iyyar da sauran kungiyoyinta sun bayyana nadin a matsayin babban tozarci ga APC.

Sun bayyana cewa Nnebe na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ya yaki APC sannan ya kira mambobinsu da sunaye kala-kala a lokacin zabe.

KU KARANTA KUMA: Matar da Sanata Abbo ya mammara ta ki gurfana a gaban kwamitin majalisar dattawa

Wadanda suka sanya hannu a jawabin daga sakatarorin APC a yankin kudu maso gabas sun hada da Kate Offor (Enugu ), Nwoba Chika Nwoba (Ebonyi) da kuma Benedict Godwin (Abia).

Pascal Otimkpu yayi Magana a madadin kungiyar matasan APC a yankin kudu maso gabas, sakataren jam’iyyar APC a jihar Anambram Chukwuma Agufugo yayi Magana a madadin jam’iyyarsa, yayinda Madukaife Okelo yayi Magana a madadin sakatarorin kudu maso gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel