A karon farko jam'iyyar PDP ta roki shugaba Buhari wata alfarma

A karon farko jam'iyyar PDP ta roki shugaba Buhari wata alfarma

- Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus ya bukaci shugaba Buhari ya sanya dokar ta baci a fadin kasar nan

- Secondus ya bayyana cewa hakan ita ce hanya guda daya tal da ta rage da za a iya kawo karshen matsalar tsaro a kasr nan

- Ya kuma bukaci shugaban kasar ya tsaya yayi nazari akan wasikar da Obasanjo ya aika masa da idon basira kuma yayi amfani da ita wajen kawo karshen kashe-kashen da ake yi a Najeriya

Babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya sanya dokar ta baci a kasar nan domin kawo karshen matsalar tsaro da kasar ke fuskanta shekara da shekaru.

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince uche Secondus, shine ya roki shugaban a lokacin da yake hira da manema labarai jiya Talata a babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban jam'iyyar yayi wannan magana ne a lokacin da yake mai da martani akan budaddiyar wasikar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya aikawa shugaba Buhari. Secondus ya ce shawarar da tsohon shugaban kasar ya bayar tayi, idan aka yi la'akari da yadda matsalar kashe-kashe ke karuwa a kasar nan.

Yayi magana akan kisan 'yar gidan shugaban Yarabawa Funke Olakunrin. Secondus ya ce matsalar tsaro daga watan Afrilu zuwa yanzu ya sanya dole manyan kasar nan su fito suyi magana akan lamarin.

KU KARANTA: Wasikar Obasanjo: Ba a bari mu gana da Buhari mu bashi shawara, shi yasa muke yawan kalubalantar shi - Bafarawa

Wadannan manyan kasa, a cewar shi, sun hada da, tsohon shugaban kasa Obasanjo, babban Faston Katolika na Abuja, John Cardinal Onaiyekan, Wole Soyinka da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa. Secondus ya bayyana wasikar Obasanjo a matsayin gaskiyar da bai kamata a juya mata baya ba, idan har ana so a kawo karshen matsalar tsaron.

Secondus ya ce jam'iyyar PDP ta na zaune da 'yan Najeriya da zuciya daya ne, "Jam'iyyar PDP ta na bukatar shugaba Buhari yayi nazari akan shawarar sanya dokar ta baci, sannan kuma ya tsaya yayi amfani da shawarar da Obasanjo ya bayar a wasikar shi."

Secondus ya ce kashe Mrs Olakunrin shine babban kisa da aka yi a kasar nan. "Kwata-kwata bai dace ba ace a kasa irin Najeriya tsohuwa 'yar shekara 94 tana zaman makokin 'yarta mai shekara 58 a duniya. Wannan ba ita ce kasar da muke mafarki ba a rayuwar mu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel