Wasikar Obasanjo: Ba a bari mu gana da Buhari mu bashi shawara, shi yasa muke yawan kalubalantar shi - Bafarawa
- Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa yayi wata magana akan wasikar da Obasanjo ya aikawaBuhari
- Ya ce shi a ganinshi ba aibu bane dan tsohon shugaban kasa Obasanjo ya aikawa da Shugaba Muhammadu Buhari wasika
- Ya ce a matsayin Obasanjo na tsohon shugaban kasa, kuma dattijon kasa yana da damar ya bayyana ra'ayinsa akan halin tsaron da Najeriya ke ciki
A wata tattaunawa da yayi da BBC, Bafarawa ya bayyana cewa, tsohon shugaban kasa Obasanjo ba kowa ya aikawa da takarda ba sai Buhari.
A matsayin Obasanjo na dattijo, dan Najeriya, kuma tsohon shugaban kasa yana da ikon ya fito ya bayyana ra'ayinsa dangane da matsalar tsaro da kasar nan ke ciki, sannan kuma ya bayar da shawarwarin da suka dace.
KU KARANTA: Kyawun tafiya dawowa: Bayan shekaru 12 da rasuwar mijinta jaruma Hafsat Shehu ta dawo harkar fim
Tsohon gwamnan jihar Sokoton ya bayyana cewa kamata yayi shugaba Buhari ya tsaya ya fuskanci inda wasikar Obasanjon ta nufa, ya dauki abubuwan da suke na gaskiya ya watsar dana watsarwa.
Bayan haka kuma Bafarawa ya bayyana cewa dalilin da yasa manyan kasar ne ke fitowa suna kalubalantar Buhari akan yadda yake tafi da gwamnatinsa, maimakon su dinga bashi shawarar sirri tsakaninsu da shi, saboda ba a bari su ganshi idan sun nemi ganawa dashi.
A cikin wannan makon ne tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya aikawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari wata doguwar wasika, inda ya nuna mashi halin da gwamnatinsa ke ciki ya kuma bashi shawara akan mafita.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng