Haka Allah ke lamarinsa: Ta samu mijin aure da kyautar kujerar Makkah saboda soyayyar da take yiwa Abba Gida-Gida

Haka Allah ke lamarinsa: Ta samu mijin aure da kyautar kujerar Makkah saboda soyayyar da take yiwa Abba Gida-Gida

- Daga rubuta sunan Abba Gida-Gida a jikin Hijabinta na makaranta, wata daliba ta zama abin kwatance a jihar Kano, musamman wajen 'yan Kwankwasiyya

- Yanzu haka dai mutane 'yan kungiyar Kwankwasiyya suna ta faman tururuwar zuwa wajen yarinyar don bata kyaututtuka

- A cikin kyautukan da aka bai wa dalibar hadda kujerar zuwa Makkah ta Umara da kuma wani saurayi da ya nuna ra'ayin a shirye yake ya aureta idan ta kammala karatunta

Siyasar jihar Kano ta canja wani sabon salo, bayan wata yarinya dalibar makarantar sakandare ta rubuta sunan dan takarar gwamna na babbar jam'iyyar adawa ta PDP na jihar Kano, Abba Kabir Yusuf (Gida-Gida) a jikin hijabinta na makaranta a daidai lokacin da take rubuta jarrabawar karshe ta fita daga sakandare.

Rubuta wannan suna ke da wuya ya bazu a shafukan sada zumunta, musamman shafin Facebook, hakan yasa wadanda suke da akidar kungiyar Kwankwasiyya a jihar suka dinga bin layi wajen bawa dalibar kyaututtuka na musamman ciki kuwa hada kujerar zuwa Makkah ta Umara.

KU KARANTA: Cin amana kiri-kiri: Kotu ta tsare Adama wacce tayi yunkurin kwacewa babbar aminiyarta miji a jihar Kaduna

Sannan wani dan kungiyar ya nuna ra'ayinsa na auren yarinyar idan ta kammala karatunta. Yanzu haka dai budurwar ta zama abar sha'awa da kwatance a wajen 'yan Kwankwasiyya saboda wannan rubutu da tayi a jikin Hijabi nata.

Abba Gida-Gida shine dai wanda ya lashe zaben jihar Kano a karo na farko kafin a soke zaben, sai kuma a karo na biyu da ake tunanin cewa jam'iyyar APC mai mulki ta tafka magudi a zaben da aka yi a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng