Allah daya gari ban-ban: Kasar da ake farautar zabiya ana sayar da sassan jikinsu tamkar na dabbobi (Hotuna)

Allah daya gari ban-ban: Kasar da ake farautar zabiya ana sayar da sassan jikinsu tamkar na dabbobi (Hotuna)

- A kasar Tanzaniya, an yarda cewa zabiya suna da kashin arziki, hakan ne yasa ake farautar su ana sayar dasu

- Rahotanni sun nuna cewa mutanen kasar suna sayar da sassan jikin zabiya, kamar yadda ake sayar da na dabba

- A cewar jaridar Daily Mail, wasu iyayen ma suna daukar 'ya'yansu su sayar saboda su samu kudi

- Mutanen da suke sayen sassan jikin zabiyan an yarda cewa sune masu kudi a fadin kasar

Zabiya a kasar Tanzaniya koda yaushe suna cikin fargaba da tsoron kada a kama su a sayar a cikin kasarsu. Sabo son kudi da mulki da mutanen kasar suke dashi yasa suke farautar zabiya suna sayarwa saboda wani imani da suke dashi a kansu.

Allah daya gari ban-ban: Kasar da ake farautar zabiya ana sayar da sassan jikinsu tamkar na dabbobi (Hotuna)
Allah daya gari ban-ban: Kasar da ake farautar zabiya ana sayar da sassan jikinsu tamkar na dabbobi (Hotuna)
Asali: UGC

Zabiya sune mutanen da ake haifarsu fari fat, daga fatarsu, gashin jikinsu da idonsu duka farare.

A kasar ta Tanzaniya sun yadda cewa sassan jikin zabiya yana kawo arziki da kuma sa'a ga mutane, saboda haka ne yasa suke farautarsu tamkar dabbobi suna sayarwa.

A cewar jaridar Daily Mail, wasu masu kudin suna sayen cinya guda akan kudi naira miliyan daya da rabi, sannan suna sayen jikin gaba daya akan kudi naira miliyan 22.

A yanzu saboda wannan imani da mutanen kasar suke dashi, yasa iyaye kan iya daukar dansu ko 'yarsu suje su sayar saboda su samu kudi.

KU KARANTA: Babbar magana: Dan Allah ku taimaka mini ina neman mijin aure na gari amma mai kudi - In ji wata budurwa

Ko da bayan mutuwarsu ne zabiya basu ba, saboda ana zuwa a bude kabarinsu a fito dasu a dinga sayarwa, rahotanni sun nuna cewa yanzu haka an bude kaburbura guda goma sha shida na zabiya.

Wani zabiya mai suna Mwigulu Matonange ya bayyana cewa ya rasa hannu dayansa ne lokacin da yake dan shekara 10. Ya ce wasu mutane biyu sun tare shi sun yanke masa hannu suka gudu cikin daji da hannun.

Allah daya gari ban-ban: Kasar da ake farautar zabiya ana sayar da sassan jikinsu tamkar na dabbobi (Hotuna)
Mwigulu
Asali: UGC

A yanzu da lokacin zabe ya gabato a kasar Tanzaniya, Zabiya sun shiga wasan buya da mutanen kasar. A bayyana cewa a lokacin zabe an fi kashe zabiya saboda 'yan siyasa sun yadda cewa zasu iya samun sa'a dasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel