Kurunkus: Motata ce Adam A. Zango ya zabga muku karyar cewa ya saya miliyan 23 - Zulaihat Ibrahim

Kurunkus: Motata ce Adam A. Zango ya zabga muku karyar cewa ya saya miliyan 23 - Zulaihat Ibrahim

- Fitacciyar 'yar wasan Hausan nan Zulaihat Ibrahim ta tona asirin Adam Zango akan motar da ya bayyana cewa ya saya miliyan 23

- Zulaihat wacce aka fi sani da Zpreety ta bayyana cewa wannan magana ba haka take ba, inda ta ce mota dai tata ce ta ara masa

- Ta kara da cewa ta yi hakan ne domin ta nunawa duniya yadda take girmama Adam Zango, amma kuma sai ya buge da yiwa mutane karya

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, wacce tauraruwarta ke haskawa a masana'antar Kannywood, Zulaihat Ibrahim, wacce aka fi sani da Zpreety, ta yi wata muhimmiyar magana akan motar da Adam Zango yace ya saya naira miliyan 23.

Zulaihat ta bayyana cewa motar nan da Adam Zango ya dinga sanyawa a kafafen sada zumunta ba tashi bace motarta ce.

Ta bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya dinga yawo a kafafen sada zumunta, inda aka nuno ta a tsaye kusa da motar tana magana.

KU KARANTA: Shikenan: Saboda biyan bukatar aljihun mu kawai muke yin wasan Hausa - Suleiman Bosho

Ga abin Zulaihat din ta ce:

"Mutane na taa tambaya ta cewa dana sami kudin wakar babban yaro mai nayi dashi, gaskiya ce nake so na fada yau, motar nan da kuka gani Baba Adamu yana hawa tsakani da Allah tawa ce.

"Da aka bani ita don nake hawa, sai naga cewa yana da kyau ka girmama na gaba gareka, sai na dauka na bashi akan zai hau na tsawon wata biyar daga nan zan karba na cigaba da amfani da motata."

A jikin bidiyon Zulaihat ta nuna asalin motar Adam Zango, domin ta kara tabbatarwa da mutane cewa motarta ce.

"Ina dai so na nunawa duniya ta san ainahin abinda ke faruwa ne saboda kowa ya san cewa karya babu kyau."

Makonnin da suka gabata ne dai hotunan jarumi Adam Zango akan wata jar mota suka dinga yawo a shafukan sada zumunta, inda aka bayyana cewa ya sayi motar naira miliyan 23.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng