Uwargida ta antaya ma mijinta tukunyar ruwan zafi a Kano saboda zai yi mata kishiya

Uwargida ta antaya ma mijinta tukunyar ruwan zafi a Kano saboda zai yi mata kishiya

Masu iya magana kan cewa son zuciya, bacin zuciya, kuma dama duk wanda ya hau dokin zuciya, zai sauka a tashar da na sani, kamar yadda wata mata take cikin halin tashin hankali da da na sani a jahar Kano bayan ta aikata ma mijinta aika aika.

Legit.ng ta ruwaito wannan matar mai suna Lauratu Ahmad ta hau dokin zuciya ne inda ta yi ma maigidanta wanka da tafasashshen ruwan zafi domin nuna rashin amincewarta da aure da yake shirin karawa.

KU KARANTA; Babban bankin Najeriya ta bayar da lasisi ga wani sabon bankin Musulunci

Wannan lamari ya auku ne a ranar Alhamis din makon data gabata, inda magidancin mai suna Aliyu Ibrahim Fayan Fayan, wanda malamin makaranta ne kuma mazaunin karamar hukumar Dambatta ya kammala shirin kara aure, amma ya ga dacewar ya sanar da matarsa.

Baya ga sanar da matar tasa, Aliyu ya dan yi hubbasa har ya bata kudin toshiyar baki domin ta sayi kayayyaki, amma duk da haka bata tausu ba, inda a wannan rana na Alhamis ta mamayeshi da tukunyar tafasashshen ruwa ta watsa masa shi duka.

A sanadiyyar haka ta kona masa jiki, bayansa da kuma gabansa, sa’annan ta ranta ana kare, sai dai wani makwabcinsa ne ma ya taimaka masa ya garzaya da shi zuwa Asibiti inda ya samu kulawa.

Sai dai da yake zakaran da Allah Ya nufa da cara, ko ana mazuru ana shaho sai ya yi, Allah Yasa Malam Aliyu bai mutu ba, kuma tuni Yansanda suka cika hannu da uwargida Lauratu, tare da gudanar da bincike akanta da shirin gurfanar da ita gaban kuliya manta sabo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel