Shikenan: Saboda biyan bukatar aljihun mu kawai muke yin wasan Hausa - Suleiman Bosho
- Suleiman Bosho ya bayyana cewa 'yan wasan Hausa na wannan zamanin suna shiga harkar ne kawai dan suka cika aljihunsu da naira
- Ya bayyana cewa yanzu babu wani kishi a cikin masana'antar fina-finan Hausa, kowa yana zuwa ne domin biyan bukatarsa
- Bosho ya kuma bayyana irin nasarorin da ya samu a harkar wasan Hausa da yake yi
A wata hira da aka yi da fitaccen jarumin barkwancin nan na fina-finan Hausa, Suleiman Bosho, a gidan rediyon freedom muryar jama'a, ya bayyana cewa: "Banbancin da ke tsakanin 'yan wasan Hausa na da dana yanzu shine, 'yan wasan da suna shiga wasan fim ne saboda kishi da cigaban yaren Hausa, amma 'yan wasan yanzu suna shiga wasan fim ne saboda su cika aljihunsu da naira."
Bosho ya bayyana cewa babbar matsalar da yake samu a harkar fim ita ce yadda mutane suka kasa fahimtar sa.
KU KARANTA: Magana ta kare: Hukumar 'Yan sanda ta bayyana yadda masu garkuwa da mutane suka kashe 'yar shugaban Afenifere
Bosho ya bayyana cewa lokuta da dama idan ya gamu da mutane sai su dinga tunanin zai yi musu irin abubuwan da yake yi a fim, bayan kuma komai da lokacinsa.
A bangaren irin cigaban da ya samu kuwa Bosho ya bayyana cewa: "Ina godiya ga Allah domin naje wuraren da ban taba tunanin zanje ba, na mallaki abinda ban yi tunanin zan mallaka ba."
A karshe ya bayyana cewa babban burinsa shine ya ga masana'antarsu ta Kannywood tana gogayya da sauran masana'antun fim na duniya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng