Buhari ya dira jihar Kaduna domin hallartan bikin yaye sojoji (Hotuna)

Buhari ya dira jihar Kaduna domin hallartan bikin yaye sojoji (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya isa sansanin sojojin saman Najeriya (Air Force Base) da ke jihar Kaduna a yau Asabar 13 ga watan Yulin shekarar 2019.

Buhari ya ziyarci jihar Kaduna ne domin bikin yaye manyan hafsoshin sojoji da ke karo na 41 a Makarantar Horas da Sojoji da ke Jaji a Kaduna.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufai, da mataimakiyarsa, Dakta Hadiza Balarabe da Tsohuwar Ministan Kudi, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed suna daga cikin wadanda suka tarbi shugaban kasar a sansanin sojojin sama da ke Kaduna.

DUBA WANNAN: Za a biya tsohon gwamnan PDP da ke gidan yari N151.1 a matsayin kudin fansho

Sauran wadanda ke cikin tawagar tarbar shugaban kasar sun hada da Sanata Uba Sani mai wakiltan Kaduna Ta Tsakiya da Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Kaduna, Muhammad Abdullahi (Dattijo) da wasu manyan jami'an gwamnatin jihar.

Ga hotunan irin tarbar da aka yi wa shugaban kasar:

Buhari ya hallarci taron yaye sojoji a Kaduna (Hotuna)
Shugaba Buhari da Gwamna Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Buhari ya hallarci taron yaye sojoji a Kaduna (Hotuna)
Gwamna El Rufai da mataimakiyarsa Hadiza Balarabe da tsohuwar Ministan Kudi Zainab Shamsuna Ahmed
Asali: Facebook

Buhari ya hallarci taron yaye sojoji a Kaduna (Hotuna)
Buhari ya sauka a Airforce Base a Kaduna
Asali: Facebook

Buhari ya hallarci taron yaye sojoji a Kaduna (Hotuna)
Karamar yarinya ta yi wa Shugaba Muhmmadu Buhari maraba da zuwa Kaduna
Asali: Facebook

Buhari ya hallarci taron yaye sojoji a Kaduna (Hotuna)
Shugaba Buhari na gaisawa da Sanata Uba Sani
Asali: Facebook

Buhari ya hallarci taron yaye sojoji a Kaduna (Hotuna)
Shugaba Buhari na gaisawa da Muhammad Abdullahi
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel