Maraya dan shekara 11 da ke sana'ar ga-ruwa a Kano ya ce baya kaunar bara (Hotuna)

Maraya dan shekara 11 da ke sana'ar ga-ruwa a Kano ya ce baya kaunar bara (Hotuna)

Wani mutum mai suna Hassan Ibrahim Gama ne ya wallafa hotuna da bidiyon Umar mai shekaru 11, da ke sana'ar ga ruwa a garin Kano.

A cewar Ibrahim, iyayen yaron sun rasu hakan yasa ya fara sana'ar sayar da ruwa saboda baya kaunar yin bara.

"Sunan yaron dan shekara 11 Umar.

Sana'ar sayar da ruwa ya ke yi a Kano. Ya kan sayar da jarkokin ruwa masu lita 25 guda 16 a kurarsa.

DUBA WANNAN: Za a biya tsohon gwamnan PDP da ke gidan yari N151.1 a matsayin kudin fansho

Umar cikakken maraya ne saboda ya rasa mahaifinsa da mahaifiyarsa amma ya ce baya kaunar bara shi yasa ya yi alkawarin yin gwagwarmayar neman halas a rayuwansa," kamar yadda Ibrahim ya rubuta.

Ma'abota amfani da shafin sada zumunta sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan batun inda wasu ke ganin ya dace ace yaron yana makaranta ne ba sana'a ba inda wasu kuma suka yi wa yaron jinjina kan jajircewarsa na yin sana'a a maimakon bara.

Ga hotunan Umar da kayan sana'arsa a kasa:

Maraya dan shekara 11 da ke sana'ar ga ruwa a Kano ya ce baya kaunar bara (Hotuna)

Umar dan shekara 11 mai sana'ar ga ruwa a Kano
Source: Facebook

Maraya dan shekara 11 da ke sana'ar ga ruwa a Kano ya ce baya kaunar bara (Hotuna)

Maraya dan shekara 11 da ke sana'ar ga ruwa a Kano ya ce baya kaunar bara (Hotuna)
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel