Wata uwargida a Kano ta antayawa mijinta ruwan zafi don zai kara aure (Hoto)

Wata uwargida a Kano ta antayawa mijinta ruwan zafi don zai kara aure (Hoto)

- Wata matar aure a Kano ta yi wa mijinta mummunan rauni

- Matar da kona mijinta da ruwan zafi saboda yana shirin yi mata kishiya

- An nemi matar an rasa bayan ta aikata wannan mummunan lamarin

Wata matar aure a jihar Kano ta wuce gona da irin wurin nuna kishin ta inda aka ce ta antayawa mai gidan ta tafashashen ruwa tayi masa mummunan rauni saboda wai zai kara aure.

Matar da aka ce sunan ta Lauratu Ahmad ta yi wa mai gidan ta, Malam Aliyu Ibrahim Fanyan-Fayan mummunan rauni da ruwan zafi domin nuna kin amincewarta da amaryar da ya ke shirin auro wa.

A cewar rahoton da Daily Trust ta wallafa, lamarin ya faru ne a karamar hukumar Danbatta na jihar Kano.

DUBA WANNAN: Za a biya tsohon gwamnan PDP da ke gidan yari N151.1 a matsayin kudin fansho

Wata uwargida a Kano ta antayawa mijinta ruwan zafi don zai kara aure (Hotuna)
Wata uwargida a Kano ta antayawa mijinta ruwan zafi don zai kara aure (Hotuna)
Asali: Instagram

An ruwaito cewa Malam Aliyu ya fadawa matarsa cewa zai auro amarya kuma ya tafi ya ba ta wasu kudade domin sayan kayan 'danne kirji' saboda auren da zai kara.

"Ban ga wani canji cikin halayen ta ba bayan da na fada mata zan karo aure, mun cigaba da zaman mu lafiya. Har ma ta ce za ta taimaka wurin sayo kayyayakin da za a saka cikin akwatin amarya," inji Malam Aliyu a hirar da ya yi da Daily Trust.

Ya cigaba da bayanin yadda ya dawo gida kum kwatsam matarsa ta antaya masa ruwan zafi.

Aliyu ya ce, "Bayan na dawo gida da dadare, na sayo musu nama. Na tarar da ita tana dafa ruwan zafi amma ban san abinda za tayi da shi ba."

Aliyu yana nan a babban asibitin garin Danbatta yana karbar magani inda ya ce suna da yara 10 da matarsa kuma yanzu ba a san inda ta shiga ba bayan aikata mummunan aikin.

Kakakin 'yan sandan jihar, ASP Abdullahi Haruna ya ce kawo yanzu ba shigar da rahoton afkuwar wannan lamarin a hedkwatan 'yan sanda ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel