'Yan sanda sun damke barayin shanu a jihar Zamfara

'Yan sanda sun damke barayin shanu a jihar Zamfara

Rundunar 'Yan sandan jihar Zamfara sun kwato shanu 281, rakumma shida, doki daya da jakunna uku da 'yan bindiga suka sace a jihar tare da kama mutane uku da ake zargi da hannu cikin satar.

Mutane ukun da aka kama sune Sa’idu Lawali, Muhammad Umaru da Shehu Umaru kuma tuni an gurfanar da su gaban kotu.

Mai magana da yawun rundunar, SP Muhammad Shehu ya ce an kamo wadanda ake zargin ne a garin Kontagora da ke jihar Niger bayan sun tsere daga Zamfara.

DUBA WANNAN: Za a biya tsohon gwamnan PDP da ke gidan yari N151.1 a matsayin kudin fansho

Ya ce gwamnan jihar, Dr Bello Muhammad ya bayar da umurnin aijye dabobin a filin cin kasuwar baje koli na jihar Zamfara.

Shehu ya kuma ce 'yan sandan sun kama wani gawurtaccen dilalin kwayoyi, Sanusi Abdulkadir da aka samu da kwayoyin Diazapan da D5 da Xzai da kuma wani ganye mai yawa da ake zargin wiwi ne.

Kakakin 'yan sandan ya ce an kama dilalin miyagun kwayoyin ne sakamakon bayanan sirri da daya daga cikin wadanda aka kama ya bayar wadda hakan yasa jami'an hukumar suka garzaya gidan wanda ake zargin da ke GRA a karamar hukumar Gusau.

A cewar Sanusi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya dade yana sayar da miyagun kwayoyi kuma nan ba da dadewa ba za a gurfanar da shi a kotu.

Ya yi kira ga mazauna jihar su cigaba da taimakawa 'yan sanda da bayyanai masu amfani da za su taimaka musu kawar da miyagu a cikin al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel