Gwamnatin jihar Kebbi ta nada tsohon gwamna Sai'du Dakin gari a matsayin Amirul Hajji

Gwamnatin jihar Kebbi ta nada tsohon gwamna Sai'du Dakin gari a matsayin Amirul Hajji

-Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya nada tsohon gwamnan jihar, Alhaji Sa'idu Dakingari a matsayin Amirul Hajji kuma shugaban wakilan alhazzai na jihar Kebbi

-A jawabin da babban sakataren yada labarai na gidan gwamnati, Abubakar Dakingari ya fitar, an bayyana babban sakataren gidan gwamnati a matsayin sakataren wakilan

A jiya Juma'a 12 ga watan Yuli 2019, gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya nada tsohon gwamnan jihar, Alhaji Sa'idu Dakingari a matsayin Amirul Hajji kuma shugaban wakilan alhazzai na jihar Kebbi a Hajjin 2019

A jawabin da babban sakataren yada labarai na gidan gwamnati, Abubakar Dakingari ya fitar, an bayyana babban sakataren gidan gwamnati a matsayin sakataren wakilan.

A jawabin, an zayyana sauran wakilan da suka hada da tsohon ministan wasanni da harkokin kasashen waje Dr. Sa'idu Sambawa, tsohon ministan kimiyya da fasaha Farfesa Abubakar Ka'oje da tsohon ministan wasanni Alhaji Bala Bawa Ka'oje.

KARANTA WANNAN: Zan sauke duk kwamishinan da ya gagara yin aikinsa – El-Rufa’i

Saura sun hada da; tsohon mataimakin kwantirola na hukumar kwastam, Alhaji Salisu Namagare, tsohon ministan harkokin kasashen waje Alhaji Buhari Bala da kuma mukaddashin alkalin alkalai na jihar Jastis Suleiman Ambursa da dai sauransu.

A ranar Laraba 10 ga watan Yuli 2019, Legit.ng ta ruwaito cewa jirgin farko na alhazzan Najeriya ya tashi dauke da maniyyata daga jihar Katsina.

Hakan ya biyo bayan kammala shirye shirye da ga wakilan hukumar jin dadin alhazzaita kasa (NAHCOM). Wakilan hukumar su 39 sun yi gaba zuwa kasa mai tsarki tun ranar juma'a 5 ga watan Yuli 2019.

Haka zalika jami'an lafiya su 15 karkashin jagorancin Dr. Ibrahim Kana sun riga sun hallara kasar Saudiyya don gabatar da ayyukan lura da lafiyar maniyyata aikin Hajjin.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel