Abin da mamaki: Wata mata ta shekara uku tana kwana da gawar mahaifiyarta a daki

Abin da mamaki: Wata mata ta shekara uku tana kwana da gawar mahaifiyarta a daki

- An gano gawar wata mata a wani gida da 'yarta ta ajiyeta na tsawon shekara uku ba tare da ta bari an binne ta ba

- Yanzu haka dai an cafke matar da ta ajiye gawar, wacce suke zaune a cikin gidanta ita da 'yarta mai shekaru 15 a duniya

- Yanzu dai mahaifiyar yarinyar na iya fuskantar zaman gidan kaso na tsawon shekaru tare da tara mai yawa

An cafke wata mata a jihar Texas ta kasar Amurka, yayin da aka gano cewa tana ajiye da gawar mahaifiyarta a cikin gidanta wanda yakee dauke da dakuna guda biyu da suke zaune ita da 'yarta guda daya.

Jami'an 'yan sandan jihar sun bayyana cewa mahaifiyar yarinyar wacce ke da shekaru 71 ta rasa ranta ne lokacin da ta fadi a shekarar 2016.

'Yan sandan kuma sun zargi 'yar matar mai shekaru 47 da kasa taimakawa mahaifiyar tata a lokacin da ta fadi, hakan ne ya sanya matar ta mutu kwanaki kadan bayan faduwar tata.

KU KARANTA: Tashin hankali: Mu miliyan 21 ne, kuma a shirye muke mu bada rayuwarmu don ganin shugaban mu ya fito - 'Yan Shi'a

An gano kwarangwal din marigayiyar a cikin daya daga cikin dakunan biyu, inda ita kuma matar da 'yarta suke kwana a daya dakin.

Jikar matar tana da shekaru 15 lokacin da ta dinga kwana da gawar kakarta a cikin gidan. Hakan ne yasa ake tuhumar mahaifiyar yarinyar da kokarin lalata rayuwar 'yarta.

Yanzu dai an kai yarinyar tana zaune karkashin kulawar danginsu, sannan kuma tana karbar tallafi daga wajen hukumar kula da yara ta kasar Amurka.

Mahaifiyar yarinyar na iya fuskantar zaman gidan kaso na tsawon shekara 20 sannan za a ci tarar dala 10,000 daga wajenta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel