Ka dawo da shirin samar da Ruga – Kungiyar Izala ga shugaba Buhari

Ka dawo da shirin samar da Ruga – Kungiyar Izala ga shugaba Buhari

Kungiyar Izala ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ya dawo da shirin da gwamnatinsa ta dauki aniyar gabatarwa a kafa Rugar Makiyaya, domin inganta rayuwarsu.

Kiran ya fito ne daga bakin Shugaban Kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Shehun malamin da yake kiran wajen wa'azin kasa da kasa da kungiyar ta gabatar a garin Hadejia, Jihar jigawa, yace: "ba mu ji dadin yadda Gwamnatin Tarayya ta yi magana kan shirin yadda za'a samar da ruga na Fulani amma daga baya ta dakatar saboda maganar wasu mutane. Bai kamata ba.

"Ya kamata gwamnati idan ta yi magana ta tsaya a kai, ko ta ce za ta duba ta gani saboda wannan shirin zai taimaka wajen zaman lafiyar Nijeriya.

"Masu wannan magana hassada ce, a ransu shi ya sa suke sukan wannan shirin, saboda wata kila gwamnatin su ta wuce ba su yi irin wannan ba.

KU KARANTA KUMA: Yan majalisa na APC sun yi kira ga tsige Gwamna Obaseki

"Wannan shirin na Ruga wannan kungiya tana kira ga gwamnatin tarayya cewa, adawo da wannan program ayi bayaninsa al'umma su gane fa'idarsa. Kuma a dawo da shi a yi shi domin zai amfanar da zaman lafiya".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel