Za mu ci gaba da hakar mai a Arewa - Shugaban NNPC

Za mu ci gaba da hakar mai a Arewa - Shugaban NNPC

Sabon manajan darakta na Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), Mista Mele Kolo Kyari, ya bayyana cewa kamfanin zai ci gaba da binciken man fetur ba jib a gani a yankin Arewacin kasar, tare da yankin tafkin Chadi.

Mista Kyari, ya bayyana hakan ne jim kadan bayan tsohon Shugaban kamfanin, Dakta Mai Kanti Baru, ya gabatar da shi a gaban Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

An tattaro inda yake fadin cewa: “Za mu ci gaba da neman hanyoyin hako mai a yankunan Arewa da sauran yankunan kan iyakar Najeriyar.

“Muna da wuraren da har yanzu ba mu kai ga gano mai ba harma a yankin kudancin kasar, za mu bunkasa hakar mai ta yadda kowa zai amfana da gajiyar hakan shirin za mu aikata hakan, cikin yardar Allah.”

KU KARANTA KUMA: Ku yi watsi da barazanar kungiyar arewa kan Ruga – Fadar Shugaban kasa ga yan Najeriya

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, ya amince kashe biliyan N5 a makarantun gaba da sakandire na kasa domin gudanar da bincike a bangarorn ilimi daban-daban.

Hukumar sarrafa kudaden gudanar da aiyuka a makarantun gaba sakandire (TETfund) ce za ta raba kudin ga manyan makarantun.

Babban sakataren hukumar TETFund, Farfesa Suleiman Bogoro, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin rantsar da wani kwamitin da zai gudanar da rabon kudin bayan ya tantance yadda za a raba su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel