Matsalolin ma’aurata: Yadda wata mata ta kashe mijinta da budurwarsa a Legas

Matsalolin ma’aurata: Yadda wata mata ta kashe mijinta da budurwarsa a Legas

Wata mata mai suna Akorede Balogun ta kashe mijinta, Rasaki Balogun dan shekara 50, tare da buduwarsa Muyibat Alabi bayan ta kamasu suna saduwa ‘turmi da tabarya’ a gidansu dake lamba 16 titin Taiwo Oke, unguwar Ejigbo a jahar Legas.

Sai dai a kokarinta na yin basaja, sai wannan mata ta fara kiran Yansanda tana kukan cewa ta dawo gida ne kwatsam ta tarar da gawar mijin nata da budurwarsa kwance tsirara haihuwar uwarsu a tsakar dakinta, don haka take neman gano wanda ya kashesu.

KU KARANTA: Gaba kura baya sayaki: Yan ‘kato da gora’ sun kashe mutane 17 a jahar Katsina

Abinka da ramin karya, wanda masu iya magana ke cewa kurarre ne, ashe makwabcinsu mai suna Oguegbu Promise dan shekara 25 yana kallon duk abinda ya faru, kuma ya tona ma uwargida Akorede asiri a ofishin Yansanda.

Promise yace yana kallo lokacin da matar tare da wani mutumi suka dura ma mamatan biyu guba a bakunansu da karfi da yaji, amma yayin da matar ta fahimci yana kallonsu, sai ta rokeshi ya rufa mata asiri, har ma ta bashi kyautar motarta a matsayin cin hanci.

“Ina zaune a daki sai matar maigidanmu ta kirani zuwa dakinta wai zan tayata wani aiki, shigata dakin keda wuya sai na ci karo da wani katon mutum a dakin, inda ya umarceni na daure hannun maigidanmu da budurwarsa, kuma a lokacin suna ta ihu suna neman taimako, amma babu yadda na iya, a haka na daure musu hannu.

“Daga nan sai matar ta dura musu wani ruwan guba a baki, nan da nan suka mutu, sai ta juyo kaina ta bani makullin motarta a matsayin cin hanci wai don kada na fallasa abinda ya faru, abinda yasa ban kai kara ga Yansanda ba shine saboda ina jin tsoronta.” Inji Promise dan shekara 25.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel