Gwamna Bello ya karbi takardar neman izinin takarar gwamnan jihar Kogi

Gwamna Bello ya karbi takardar neman izinin takarar gwamnan jihar Kogi

A ranar Laraba 10, ga watan Yulin 2019, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya karbi takardar neman izinin sake tsayawa takarar kujerar sa.

Gwamna Bello ya mallaki takardun bayyana kudirin neman takara a babban ofishin jam'iyyar APC na kasa dake garin Abuja yayin gabatowar zaben gwamnan jihar Kogi da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamban 2020.

Kamar yadda jaridar The Nigerian ta ruwaito, gwamna Bello ya mallaki takardar bayyana kudirin takara na jam'iyyar APC a kan zunzurutun kudi na Naira miliyan 22.5. Ya kasance dan takara na farko da ya mallaki takardar sa ta neman izini.

Akwai kimanin 'yan siyasa 20 dake hankoron samun tikitin takarar gwamnan jihar Kogi a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC yayin zaben fidda gwani da za a gudanar a ranar 29 ga watan Aguusta cikin birnin Lokwaja.

Shugaban cibiyar tsare-tsare na jam'iyyar APC, Alhaji Abubakar Kari, shi ne ya gabatar da takardar neman izini takara ga gwamna Bello a hedikwatar jam'iyyar dake babban birnin kasar nan na Tarayya.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta fara kidayar dabbobi da yi masu shaida a Najeriya

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, wakilin shiyyar Kogi ta Yamma a zauren majalisar dattawan kasar nan, Sanata Dino Melaye, ya bayyana dalilin sa na neman takarar kujerar gwamnan jihar Kogi inda ya ce bai wuce tsanani kishi na tsamo jihar daga halin da take ciki.

Sanatan ya wassafa halin kunci da jihar ke fuskanta kama daga rashin biyan albashin ma'aikata,rashin tsaro, ta'addancin masu garkuwa da mutane da kuma datse makwararin romon dimokuradiyya a matsayin manyan dalilai da suka angiza shi neman jagoranci a jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel