Allah Sarki: Ina jin bani da rabon hawa kujerar gwamnar jihar Taraba - Mama Taraba

Allah Sarki: Ina jin bani da rabon hawa kujerar gwamnar jihar Taraba - Mama Taraba

- Tsohuwar ministar shugaba Buhari, Hajiya Aisha Alhassan ta kai ziyara fadar gwamnan jihar Taraba

- Ta bayyana mishi cewa ta na jin bata da rabon zama gwamnar jihar tunda har Allah bai bata ba

- Ta kara da cewa kofar ta a bude take idan gwamnan jihar yana neman wani taimako yayi mata magana

Jiya Talata ne 9 ga watan Yuli, tsohuwar ministar harkokin mata, da cigaban al'umma, Hajiya Aisha Alhassan, ta ce tana jin ba ta da rabon hawa kujerar gwamnan jihar Taraba.

Tsohuwar ministar da take magana akan shan kasar da ta yi a zaben gwamnan jihar Taraba da ya faru watannin baya, ta bayyana hakan ne a lokacin da ta kai wata ziyara ga gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku.

KU KARANTA: Tirkashi: Ba ku isa ku dakatar dani ba, saboda nima Sanata ne tamkar ku - Sanata Abbo ya gargadi Sanatoci

"Allah ne yake bayar da mulki ga wanda ya so. Zai iya yiwuwa kai kake ganin kafi cancanta da wannan mukami, amma idan Allah bai baka ba babu yadda ka iya," in ji ta.

Ta kara da cewa, "Ina jin bani da rabon zama gwamnar jihar Taraba, amma dole wani ya samu wannan kujerar.

"Zamu cigaba da goya maka baya, kuma idan akwai wani taimako da kake tunanin zamu yi maka, kofarmu kullum a bude take. Mun ji dadin zuwan mu nan, kuma muna taya ka murna da wannan mukami naka da ka samu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel