Gemu da gemu: Yadda 'yan bindigar Zamfara suka gana da sabon kwamishina 'yan sandan jihar

Gemu da gemu: Yadda 'yan bindigar Zamfara suka gana da sabon kwamishina 'yan sandan jihar

Sabon kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara, Mista Usman Nagogo, ya jagoranci tattaunawar da ta kai ga kubutar da mutane fiye da 50 da 'yan bindiga da 'yan kungiyar 'sa kai' (bijilanti) ke rike da su.

Da ya ke gudanar da wani taro da manema labarai a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, Nagogo ya bayyana cewa sulhun da sasanton da ake gudanar wa ya bashi damar gana wa da 'yan bindiga 'gemu da gemu'.

A cewarsa, 'yan bindiga da 'yansakai na da hannu a aikata laifin garkuwa da mutane a jihar Zamfara.

"Tun bayan da na kama aiki na fadi cewa zan bawa tattauna wa, domin samun zaman lafiya, muhimmanci, saboda yin hakan shine sabon salon da duniya ke ya yi a cikin aikin dan sanda. Yin hakan shine mafita, a saboda haka ya zama wajibi," a cewar sa.

Kwamishina ya kara da cewa kwamitin sulhu da aka kafa ya gudanar da zama daban-daban domin sulhunta bangarorin da ke rikici da juna.

DUBA WANNAN: Martanin rundunar soji a kan labarin maye gurbin Buratai da Adeosun

"Kamar yadda muka gudanar da taro da Y'ansakai da kungiyoyin Fulani da suka hada da Miyetti Allah, sarakunan Fulani da Ardo na kananan hukumomi 14, dukkansu sun bayyana masa rashin jin dadinsu a kan yadda amfani da gonakinsu na gado domin kiwo da kasuwanci ya gagare su a garuruwansu," a cewar Nagogo

Kazalika ya bayyana cewa sakamakon irin wannan zaman sulhu da ake yi, yanzu an samu raguwar aiyukan 'yan bindiga da kusan kaso 98% a jihar Zamfara.

Ya kara da cewa daga irin ribar da sulhun ya haifar akwai batun kubutar da mutane 51; maza da mata, daga hannun 'yan bindiga da Y'ansakai a Gidan Dawa da ke karkashin karamar hukumar Kaura Namoda da Kamarawa a karamar hukumar Shinkafi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel