Jerin sunaye: Mutum 5 da suka mallaki arzikin da ya fi kasafin kudin Najeriya

Jerin sunaye: Mutum 5 da suka mallaki arzikin da ya fi kasafin kudin Najeriya

Wani rahoto da wata kungiyar kasa da kasa mai zaman kanta Oxfam International ta wallafa ya nuna cewa har yanzu kashi 69 cikin 100 na 'yan Najeriya na fama da matsananciyar talauci na rayuwa kasa da dala 1.9 a kullum.

Rahoton ya kuma ce akwai har yanzu ana fifita maza kan mata a kasahen Afirka Ta Yamma ciki har da Najeriya.

Shugaban Oxfam na Najeriya, Constant Tchona ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a Abuja.

Duk da cewa alkallumar tattalin arziki sun nuna cewa Najeriya na samun cigaba cikin shekaru shida da suka shude, ta ce hakan abin mamaki ne saboda babu alamar cigaban tattalin arzikin a rayuwar talakawar kasar.

DUBA WANNAN: Shaidan Atiku da PDP ya basu kunya a gaban kotu

"Duk da cewa rata tsakanin masu kudi da talakawa matsalar ce da ake fama da shi a dukkan kasahen duniya, lamarin na Najeriya ya kazanta. Najeriya ce kasar da tafi yawan talakawa cikin jerin kasashe biyar na duniya masu arzikin man fetur," inji kungiyar.

Wani rahoto na Oxfam ya kuma ce mutane biyar mafi arziki a Najeriya da arzikinsu ya kai dala biliyan 29.9 ya dara kasafin kudin kasar na 2017 wanda ya kama naira tiriliyan 7.29, kimanin dala biliyan 23.97.

Sunayen mutane biyar da suka fi arziki kamar yadda jaridar Forbes ta rubuta sune:

1- Aliko Dangote

2 - Mike Adenuga

3 - Abdul Samad Rabiu

4 - Folorunsho Alakija

5 - Femi Otedola

A cikin shawarwarin da ta bayar, Oxfam ta bikaci gwamnatin Najeriya ta sake duba tsare-tsaren ta da yadda ake gudanar da mulki domin tabbatar da cewa arzikin kasar bai tsaya a hannun wasu tsiraru ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel