Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya yiwa wani manjo janar karin girma zuwa mukami daya da na Buratai

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya yiwa wani manjo janar karin girma zuwa mukami daya da na Buratai

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa wasu sojoji guda uku karin girma a Yau Talatar nan da yamma

- Shugaban kasar ya yiwa Manjo Janar Lamidi Adeosun karin girma zuwa mukamin Laftanal Janar

- Yanzu haka dai mukamin da aka bai wa Lamidi daya yake da mukamin shugaban sojojin Najeriya na kasa Lt-Gen. Tukur Buratai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa Manjo Janar Lamidi Adeosun karin girma daga mukaminsa zuwa mukamin Laftanal Janar (Lieutenant General).

Da karin girman da shugaban kasar yayi masa, yanzu haka dai sojan yana da mukami daya da shugaban hafsoshin soji na kasar nan Lt-Gen. Tukur Buratai.

Bayan shi, shugaban kasar ya yiwa Birgediya Janar Bulama Biu karin girma daga mukaminsa zuwa mukamin Manjo Janar.

Karin girman ya fito ne a wata sanarwar da ta fito yau Talatar nan da yamma daga bakin kakakin hukumar sojin ta kasa, Col. Sagir Musa.

KU KARANTA: Tirkashi: Munanan abubuwa guda 12 da iya 'yan arewa ne kawai suke yi a Najeriya - Fani Kayode

A cewar Musa, Buhari yana cigaba da nuna goyon bayanshi ga hukumar soji ta kasar nan, domin ganin sun kawo karshen matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar nan, musamman a yankin arewa maso gabashin kasar.

Haka kuma shugaban kasar ya karawa Laftanal AJ Danjibrin wanda ke jagorantar bataliya ta 211 dake Bauchi, zuwa mukamin Kyaftin.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taya sojojin da suka samu karin girman murna ta musamman, inda ya roke su akan su cigaba da kokarin da suke yi, domin su zama abin kwatance a cikin 'yan uwansu.

"Haka kuma, shugaban hukumar soji na kasa, Lt-Gen. Tukur Yusuf Buratai, ya taya sojojin murna, sannan yayi musu addu'ar samun cigaba a rayuwarsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel