Babbar magana: Sarkin Kano ne ya tunzura matan arewa suke kashe mazajensu - Hon. Zulyadaini Sidi Karaye

Babbar magana: Sarkin Kano ne ya tunzura matan arewa suke kashe mazajensu - Hon. Zulyadaini Sidi Karaye

- Hon Zulyadaini Sidi Mustapha Karaye, ya bayyana cewa Sarkin Kano ne ya tunzura matan arewa suke kashe mazajensu

- Idan ba a manta ba akwai wani lokaci da Sarkin ya bayyana cewa duk macen da mijinta ya mareta ta ramma

- Ya bayyana cewa bai kamata a nuna wa mata cewa matsayi daya suke da maza ba saboda raunin da Allah yayi su dashi

Idan ba a manta ba kwanakin baya an samu wani babban basarake na daya daga cikin manyan Sarakunan kasar Hausa na Musulunci, wanda yake da ra'ayi irin na 'yan boko aqeeda, ya bayar da fatawar cewa duk matar da mijinta ya mareta ta cire hannu ta rama.

Wannan Sarki yana daya daga cikin masu ra'ayin ganin an daidaita tsakanin maza da mata, a lokacin da yayi wannan maganar duk kafafen yada labarai na kasar nan sai da suka yada labarin.

A matsayinsa na Sarki uban al'ummah bai kamata ya fadi haka ba, domin kuwa kofar gabatar da barna ya bude, wanda a yanzu haka ake ganin sakamakon abin.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Har yanzu ni cikakken dan jam'iyyar APC ne - Buba Galadima

Iyaye mata tunaninsu ba iri daya bane dana maza, suna da matukar rauni ta bangaren da ya shafi tunani, idan ran mace ya baci babu abinda ba zata yi ba, yayin da shi kuma namiji a wannan lokacin zai iya danne zuciyarshi.

Kuskure ne babba a nuna wa mata cewa daya suke da maza, har kuma a basu fatawar cewa duk wacce mijinta ya mareta ta rama.

Saboda haka muna kira ga duk wasu masu ra'ayi na boko aqeedah, da su gane girman hatsarin da suke kokarin jefa mutane ciki, kullum tunaninsu shine su canja hukuncin da Allah ya gindaya, Allah ne ya hallice mu yafi mu sanin dalilin da ya sanya ya shar'anta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel