Babban Faston Najeriya ya yi kira ga Buhari ya yi murabus daga kujerar shugaban kasa

Babban Faston Najeriya ya yi kira ga Buhari ya yi murabus daga kujerar shugaban kasa

Wani babban faston cocin Anglican na Najeriya, kuma shugaban cocin a yankin Neja Delta, Tunde Adeleye ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mukaminsa saboda gazawarsa ta bayyana a fili.0

Jaridar Daily Trust ta ruwaito faston ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da huduba a cocinsa, inda yace shugaba Buhari ya gaza hada kan yan Najeriya, kuma ya gagara samun cikakken goyon bayan mafi yawan yan Najeriya, don haka babu bukatar cigaba da zamansa a kujerar shugaban kasa.

KU KARANTA: Gwamna Badaru Talamiz ya halaraci gangamin wa’azin kasa na Izala

Sai dai Faston ya daura laifin hakan akan hadiman shugaban na kusa, wanda yace sune suke yi masa ingiza mai kan turuwa, suna masa tamkar kasa na cikin lafiya, alhali kuwa abubuwa sun tabarbare a kasar.

“Idan da zan yi gaba da gaba da Buhari a, zan fada masa gaskiya tsurarta, cewa ya kamata yayi murabus daga kujerarsa saboda ya gaza, kuma hakan ya faru ne sakamakon yaudararsa da hadimansa suke yi, abubuwa sun lalace kasar nan, kowa na kokawa.” Inji shi.

Faston ya yi gargadin idan har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cigaba da amfani da shawarwarin hadimansa, tabbas Najeriya zata wargaje. Haka zalika faston ya nemi a sake komawa kan teburi domin tattauna batun raba Najeriya, saboda haka ne zai kawo zaman lafiya a Najeriya.

A wani labarin kuma, gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta lalubo sababbin hanyoyin samun makudan kudaden shiga guda 22 da zasu maye gurbin man fetir, inji shugaban hukumar habbaka fitar da kayan kasuwanci daga Najeriya, NEPC, Segun Awolowo.

Awolowo ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin da yake ganawa da manema labaru a fadar gwamnati bayan wata ganawa da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng