ASUU ta gargadi gwamnatin Najeriya a kan muhimmancin inganta harkokin ilimi
Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU, ta yi kira da babbar murya na neman gwamnatocin kasar nan da su mike tsaye wajen bayar da fifiko da kuma muhimmancin gaske a fannin inganta harkokin ilimi.
ASUU ta yi kira ga dukkanin matakan gwamnatin akan nuna cewar bai wa harkokin ilimi muhimmanci shi ne ka-in da la-in wajen assassa tubalin ci gaban kasar nan.
Shugaban kungiyar Farfesa Biodun Ogunyemi, shi ne yayi wannan kira na jan hankali yayin ganawar sa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na kasa a ranar Asabar cikin birnin Awka na jihar Anambra.
Farfesa Ogunyemi cikin takaici da kuma mamaki, ya ce tun bayan dawowar kasar nan kan tsari na dimokuradiyya tsawon shekaru ashirin da suka gabata, babu wata gwamnati ko guda da ta fita zakka wajen nuna rashin juya bayan ta akan daukaka daraja da kuma nasabar ilimi a kasar nan.
Yake cewa wannan akida ta nuna halin ko in kula da gwamnatin kasar nan ta dabbaka a kan harkokin ilimi, ya sanya jami'o'in kasar nan suka kasance kara zube ba tare da iya gogayyar kafadar su da ta sauran jami'o'in duniya da a halin yanzu ba za su iya daga yatsa a cikin sahun su ba.
KARANTA KUMA: Budurwa ta kashe dan uwanta saboda ya hana su yin fati a Kano
Kamar yadda Farfesan ya bayyana, miyagun ababe da kuma kalubalai masu barazana da yiwa kasar nan zagon kasa da suka hadar da rashin tsaro, ta'addanci, ta'ammali da miyagun kwayoyi, da kuma tabarbarewar tattalin arziki na da babbar nasaba da rashin inganci ilimi a kasar nan.
Kazalika, yayin gabatar jawaban sa a birnin Awka, Farfesa Ogunyemi ya kirayi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta gaggauta sakin ragowar kudaden kungiyar su ta malamai kamar yadda suka kulla yarjejeniya da ita tun a watan Fabrairun da ya gabata.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng