Ga irinta nan: Zuwan Nicki Minaj kasar Saudiyya zai bar baya da kura
- Ranar Larabar nan ne da ta gabata, kasar Saudiyya ta gayyaci shahararriyar mawakiyar nan mai suna Nicki Minaj
- Wannan lamari ya jawo kace-nace matuka a ciki da wajen kasar, inda kowa ya dinga tofa albarkacin bakinsa game da lamarin
- Nicki Minaj za ta gabatar da wasan nata a ranar 18 ga watan Yulin nan da muke ciki a birnin Jiddah
An bayyana Nicki Minaj a matsayin mawakiyar da za ta gudanar da wasa a gurin wani taro na wake-wake da raye-raye da kasar Saudiyya ke yi duk shekara, wannan lamari ya jawo hayaniya kwarai da gaske a ciki da wajen kasar.
Fitacciyar mawakiyar za ta gudanar da wasan nata ne a birnin Jidda, ranar 18 ga watan Yuli nan da muke ciki.
Gayyatar nata da kasar ta yi na daya daga cikin irin sauye-sauye da kasar Saudiyya ke samarwa akan harkar nishadi a kokarin da take yi na ganin ta jawo hankalin masu yawon bude ido suna kawo ziyara kasar.
KU KARANTA: Abinda ya faru a shari'ar Abba Gida Gida da Ganduje yau a kotu
Sunan mawakiyar 'Nicki Minaj' yana daya daga cikin sunayen da suka yi fice a shafin sada zumunta na Twitter ranar Larabar nan da ta gabata, a lokacin da mutane ke ta tofa albarkacin bakinsu game da sanarwar.
Wani mutumi cewa yayi, "Da ace yanzu na tashi daga dogon suman dana yi kawai sai naji ance Nicki Minaj za ta yi wasa a Saudiyya, to zan dauka ba duniyar da nake da bace na dawo."
Shi kuma wani cewa yayi, anya an tambayi shafin google game da Nicki Minaj kafin a gayyato ta:
Wannan sassauci kan harkar nishadantarwa da kasar Saudiyya ke yi wani sashe ne na shirin da Yariman kasar mai jiran gado, wato Mohammed bin Salman yake yi na ganin ya fadada harkar tattalin arzikin kasar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng