Abinda ya faru a shari'ar Abba Gida Gida da Ganduje yau a kotu
- A yau ne aka sake zaman sauraron karar Abba Gida Gida da gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje
- Jam'iyyar PDP ita ce ta shigar da karar, wacce suke zargin cewa jam'iyyar APC ta yi magudi a zaben da aka gabatar a jihar
- Yanzu dai alkalin kotun ta daga sauraron karar har zuwa ranar 13 ga watan Yuli na shekarar 2019
Bayan cigaba da sauraron korafi da mai shari'a Halima Shamaki tayi a zaman kotun yau tsakanin bangarori guda biyu na masu shigar da kara na jam'iyar PDP, da kuma bangaren da ake kara na jam'iyar APC.
Yanzu haka dai mai shari'a Halima Shamaki ta dage cigaba da sauraran wannan kara har zuwa ranar 13 ga watan Yuli, 2019 domin cigaba da sauraron karar.
Zuwa yanzu dai kotun farko ta sauraron karar zabe tana da sauran kwanaki 90 kafin wa'adin da aka dibar mata na wata shida ya cika wanda dole ne ta yanke hukunci a cikin wannan kwanaki 90 din, kamar yadda dokar kasa ta gindaya.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: 'Yan Bindiga sun kashe mutane 15 a Katsina
Sannan bayan nan akwai kotun daukaka kara wacce duk wanda rayi rashin nasara tsakaninsu zai iya daukaka kara a kotun, wacce ke jihar Kaduna, ita kuma wannan kotun doka ta bata watanni biyu ne kacal, wanda dolene ta yanke hukunci a cikin wannan kwanaki sittin.
Sai kotu ta uku wato kotun koli, tsakanin Ganduje da Abba duk wanda yayi rashin nasara yana da damar ya kara daukaka kara zuwa kotun koli wacce alkalai bakwai suke jagoranta daga ita duk wanda yayi nasara shine zai zama gwamnan jihar Kano.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng