Luwadi da yara kanana: Kotu ta yanke wa Haruna daurin shekaru 14 a kurkuku

Luwadi da yara kanana: Kotu ta yanke wa Haruna daurin shekaru 14 a kurkuku

Wata babbar kotu, da ke zamanta a Dutsen jihar Jigawa, ta yanke wa wani matashi, Haruna Abdullahi, mai shekaru 28, hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari bayan samunsa da aikata laifin luwadi da kananan yara a garin Ringim.

Mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa Haruna ya aikata laifin ne a shekarar da ta gabata a unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Ringim.

Ya kara da cewa Haruna na yaudarar yaran unguwa da alawar cokoleti zuwa dakinsa domin ya yi lalata da su.

A cewar mai gabatar da karar, dubun mai laifin ta cika ne bayan ya yaudari wani yaro da ke aji shida a makarantar firamare tare saduwa da shi ta dubura.

DUBA WANNAN: Bidiyo: Na kashe mutane fiye da 50, na samu kudi kusan miliyan N700 a cikin shekara daya- Mai garkuwa da mutane

An fara shigar da korafi a ofishin 'yan sanda na garin Ringim bayan an kama shi, sannan an kai yaron da ya yi lalatar da shi zuwa asibiti domin duba lafiyarsa.

Bayan an karanto tuhumar da ake yi masa, mai laifin ya amsa laifinsa a gaban kotun tare da neman a yi masa sassauci wajen yanke hukunci.

Alkalin kotun, Usaini Ahmad Taura, ya ce Haruna ya aikata laifi mai girma a bisa tsarin dokar Najeriya, tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.

Mai shari'a Usaini ya bayyana cewa hukuncin zai zama gargadi ga masu aikata halayya irin ta Haruna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng